ZULAI DALHAT LILISCO |
Tsohuwar jarumar Kannywood Zulai Dalhat wacce aka fi Sani da Zulai Lilisco ta rasu a sakamakon rashin lafiya. Wanda kuma tuni aka yi janaizar ta kamar yadda addini ya tanadar.
Fitaccen jarumi kuma shugaban Hukumar tace finafinan Kannywood Abba Al-Mustapha ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook kamar haka.
"INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN
Allah yayi wa ZULAI DALHAT LILISCO, mata ga dan Uwa kuma Jarumi Shuaibu Lilisco kuma tsohuwar jaruma a masana’artar KANNYWOOD bayan fama da rashin lafiya. Zaayi Jana’izarta yanzu a unguwar TUDUN YOLA.
Muna Addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata Kurakuranta yasa Aljanna ce makomarta. Idan Tamu Tazo kuma Allah yasa mu çıka da kyau da İmanı.
R.I.J.F 😭😭😭😭😭"
ZULAI DALHAT LILISCO |
Muna addu'ar Allah ya jikan ta da Rahama ya baiwa iyalanta hakurin jure rashin ta amin.