Wata mata ta rasa ranta ana tsaka da kara mata duwawu
![]() |
Wata mata ta rasa ranta ana tsaka da kara mata duwawu |
Wata mata mai shekara 36 mai suna Madam Abiola, ta rasu a lokacin da ake mata tiyatar ƙara girman ɗuwawu a wani asibiti da ke unguwar Lekki a Legas.
Aminiya ta rawaito marigayiyar ta fara haki jim kaÉ—an bayan da wata ma’aikaciyar jinya ta yi mata allurar a asibitin.
Jami’in hulÉ—a da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an kama ma’aikaciyar jinya da ta yi wa marigayiyar allura.
Hundeyin ya ce lamarin wanda direban marigayiyar ya kai rahoto a ofishin ’yan sandan ya faru ne a ranar 27 ga Agusta, 2024.
Ya ce, wani direba ya kai rahoto a ofishin ’yan sanda na Maroko cewa da misalin Æ™arfe 3:00 na rana, wacce yake yi wa aiki mai shekaru 36 a Diamond Estate da ke unguwar Sangotedo da ke Ibeju-Lekki ta buÆ™aci ya kai ta wani asibitin da ke Lekki Phase 1. don allurar BBL don Æ™ara girman É—uwawu.
“Ya yi iÆ™irarin cewa da isowar mai asibitin ya umarci wata ma’aikaciyar jinya da ta yi matar allurar, daga nan sai Abiola ta sume ta fara haki, inda ya yi iÆ™irarin cewa an yi yunÆ™urin ceto Abiola ne kuma aka garzaya da ita zuwa asibitin Lekki Phase 1 fon duba lafiyarta sai Likitan ya tabbatar da rasuwarta.
“Bisa rahoton, ’yan sanda daga ofishinsu sun ziyarci wurin da aka duba gawar, an ajiye gawar a É—akin ajiyar gawarwaki, an kama ma’aikaciyar jinyar,” in ji shi.
Leave Comments
Post a Comment