Tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Umar, ta kwanta dama a gidan mijin ta

Tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Umar, ta kwanta dama a gidan mijin ta
Zainab Umar


ALLAHU Akbar! Allah ya yi wa jaruma a Kannywood, Zainab Umar, rasuwa.


Zainab ta rasu a daren jiya Alhamis, 5 ga Satumba, 2024 da misalin karfe 8:00 a gidan mijin ta da ke Layin 'Yan Kifi, Rigasa, Kaduna, bayan fama da ciwon ciki na kwana biyu.


Zainab ta na daya daga cikin 'ya'yan kamfanin shirya finafinai na Gidaje Films da ke Tudun Wada, Kaduna.


Shugaban kamfanin, Sabi'u Muhammad Gidaje, ya shaida wa wakilin mu cewa, "Zainab ta taba aure, bayan ta fito daga gidan miji ne ta shigo harkar fim. Amma da yake Allah na son ta rasu a dakin mijin ta ne, ba ta dade da komawa dakin mijin nata ba, Allah ya dauki rayuwar ta."


Wasu daga cikin finafiinan da ta fito a ciki sun hada da 'Duhun Zuciya', 'Manyan Mata', 'Fansar Waye' da 'Yan Nepa'.


Allah ya jikan Zainab da rahama, ya albarkaci dukkan abin da ta bari, amin.


Source News 

Hausa Magazine

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post