Shirye-Shirye
Gasar Mutum Mafi Muni A Kasar Zimbabwe 2024
Tuesday, August 13, 2024
0
![]() |
Gasar Mutum Mafi Muni A Kasar Zimbabwe 2024 |
Wannan shi ne karo na biyar a jere da William Masvinu ke lashe gasar mutumin da ya fi kowa muni a kasar Zimbabwe, kuma ya ce nasarar ta ba shi damar yin fice da har yake samun kudade daga tallace-tallace.
William Masvinu ya lashe gasar wanda yafi kowa muni (Mr Ugly) a daren Lahadi. Mista Ugly wata gasa ce ta shekara-shekara wacce ke fitar da sarkin munana a cewar masu shirya gasar.
Jama'a da dama ne suka halarci gasar Mr Ugly ta Zimbabwe ta 2024 domin ganin William Masvinu ya sake lashe kambun a karo na 5 a gasar.
An bashi kyautar $500 da saniya.
"Babu wanda zai iya jayayya cewa ni ne mafi muni a Zimbabwe. Yanzu ina son fitar da munina a wajen kasar. Idan akwai wanda yafi kowa muni a duniya (Mista Ugly World), ina da yakinin zan kawo kambin Zimbabwe," in ji Masvinu.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment