Takaitaccen Tarihin Jackie Chan - Android Pols

Takaitaccen Tarihin Jackie Chan

Takaitaccen Tarihin Jackie Chan 


An haifi Jackie Chan a Hongkong a ran 7 ga watan Afril na shekarar 1954 (Yanzu Yanada Shekaru 70). Ɗan wasan kwaikwayo, darekta, marubuci, furodusa, mai fasaha. Iyayensa, Charles Chan da Lee-lee Chan sun rada masa sunan Chan Kong-sang, wato sunansa na yanka, wanda ke da ma'anar "an haife shi a Hongkong". Lokacin da aka haife shi, Jackie na da nauyin pound 12, shi ya sa ba yadda za a yi sai a yi wa mahaifiyarsa tiyata.


A lokacin da yake karami, mahaifinsa ya kan tashe shi da sassafe, kuma tare za su yi wasan Kung fu. Sabo da a ganin mahaifinsa, wasan Kungfu na iya taimakawa wajen raya halayensa da kuma koya masa hakuri da karfi da kuma bajimta.


A lokacin da yake da shekaru 7 da haihuwa, mahaifinsa, Charles Chan ya kama aikin kuku da ofishin jakadancin Amurka a Australia, amma yana ganin cewa, ya fi kyau Jackie ya koyi wani abu a Hongkong, shi ya sa ya bar shi a Hongkong, don ya shiga kwalejin koyon wasan kwaikwayon kasar Sin, inda Jackie ya yi shekaru 10 yana koyon wasan Kungfu da kundumbala da waka da kuma wasan kwaikwayo.


A lokacin da yake da shekaru 17 da haihuwa, Jackie ya gama karatu a kwalejin koyon wasan kwaikwayo ta kasar Sin. Amma a lokacin, wasannin kwaikwayo na kasar Sin ba su samu karbuwa sosai ba, shi ya sa Jackie da abokan karatunsa sun sha wahalar samun aikin yi, sai dai kawai suka kama ayyukan kwadago da kasada. A lokacin, Hongkong na fitar da dimbin fina-finai a kowace shekara, kuma kullum ana bukatar samari masu aikin kasada, ga shi kuma Jackie ya kasance mutum mai kuzari da karfi da kuma hikima, shi ya sa ba da jimawa ba sai ya yi suna sabo da rashin tsoronsa a wajen ayyukan kasada.


Daga bisani, Jackie ya yi shekaru da dama yana aikin kasada. Amma ayyukan fina-finai sun fara tabarbarewa a Hongkong, shi ya sa ba yadda zai yi sai ya kaura zuwa Australia domin zama tare da iyayensa. A lokacin da yake Australia, Jackie ya taba aiki cikin wani dakin cin abinci da kuma wurin gine-gine, kuma a can wurin ne ya sami sunan "Jackie". Wani ma'aikacin wurin ya sa masa wannan suna sabo da bai iya fada ainihin sunansa, wato "Kong-sang" sosai ba, kuma ya fara kiransa da "little Jack", wanda daga baya ya zama "Jackie".


Amma Jackie bai sami jin dadi ba a Australia. Ayyukan gine-gine na da wahala, kuma halin bai kyautata ba sai bayan da wani mutum mai suna Willie Chan ya buga masa waya. Willie Chan yana ayyukan fina-finai a Hongkong, kuma a lokacin, yana neman wani da ya taka rawa cikin wani fim da wani shahararren darektan fim na Hongkong ke yi. 


Ayyukan kasada da Jackie ya taba yi sun burge Willie sosai. Ba da jimawa ba, Jackie ya kama hanyar komawa Hongkong. Amma duk da haka, fina-finan da Jackie ya yi ba su sami nasara sosai ba, kuma dalili shi ne Jackie bai yi amfani da basirar da Allah ya ba shi yadda ya kamata ba. Har zuwa lokacin da ya nuna ra'ayoyinsa cikin fina-finai, wato hada abubuwa masu ban dariya a cikin fina-finai na Kungfu, sai ya zama wani babban tauraron fim. 


Fim mai taken "Snake in Eagle's Shadow" ya zama babbar nasara ta farko da ya samu, daga baya, akwai "Drunken Master" da "Fearless Hyena", wadanda dukansu suka sami farin jini sosai, wadanda kuma suka sa Jackie ya samu karbuwa sosai a nahiyar Asiya. Amma duk da nasarorin da ya samu a Asiya, Jackie bai yi fice sosai ba a farkon zuwansa a Hollywood. Shi ya sa ya bar Amurka, kuma ya mai da hankalinsa a kan yin fina-finai a Hongkong.


Bayan kimanin shekaru 10, Jackie ya sake zuwa Hollywood, inda ya fitar da fim mai suna "Rumble in the Bronx", wanda ya tabbatar da matsayinsa a zukatan masu kallon fim na Amurka. Daga baya, Rush Hour da Shanghai Noon dukansu sun saka Jackie cikin jerin sunayen taurari na Hollywood.


A cikin 1982, Chan ya auri Joan Lin, 'yar wasan kwaikwayo ta Taiwan. Sun haifi ɗansu da ya zama mawaƙi kuma ɗan wasan kwaikwayo Jaycee Chan. Jackie Chan kuma yana da 'yar da aka haifa a ranar 18 ga Janairun 1999 sakamakon karin aure da Elaine Ng Yi-Lei. Chan ya yarda cewa "ya aikata laifin da yawancin maza a duniya suke aikatawa". Duk da haka, Elaine ta yanke shawarar cewa za ta kula da 'yarta ba tare da Chan ba.


A shekara ta 2004, masanin fina-finai Andrew Willis ya bayyana cewa Chan watakila shi ne "tauraron fina-finai da aka fi sani a duniya." A cikin 2015, Mujallar Forbes ya kiyasta ƙimar kudin sa ta kai dala miliyan 350, kuma a cikin 2016, shi ne ɗan wasan kwaikwayo na biyu mafi girma a duniya. Kuma ya fito a fina-finai sama da 150.


Ban da fina-finai, a cikin 'yan shekarun baya, Jackie yana ta kara mai da hankali a kan harkokin jin dadin al'umma. Ya kasance jakadan UNICEF da kuma UNAIDS, kuma ya yi lokuta da yawa yana tare da yara da kuma wadanda ke bukatar taimakon sauran jama'a.


Chan dan addinin Buddah ne, amma baya son magana akan Imaninsa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post