Hanyoyin da za su taimaka wurin daɗewa a kwanciyar aure

41-Year-Old Professor Takes Charge of UniAbuja as Na’Allah Steps Down
Hanyoyin da za su taimaka wurin daɗewa a kwanciyar aure



Kawowa da wuri shi ne lokacin da namiji ya yi inzali da wuri fiye da yadda ake tsammani ko kuma wasu lokuta (mafi yawa mintuna 2) bayan fara kwanciyar aure. Wasu lokutan inzali da wuri yana faruwa ne saboda rashin ƙwarewa, rashin shiri, rashin lafiya, ko kura-kurai da za a iya kauce wa yayin saduwa.


Wannan babbar damuwa ce ga maza da mata, saboda yana haifar da rashin gamsuwa a tsakanin ma'aurata a lokacin saduwa. Kuma mata sukan fi shan wahala da cutuwa a cikin wannan yanayi.


Shi ya sa yake da muhimmanci da kuma wajibi ga maza su shawo kan lamarin. Don matsalar tana rusa zamantakewa a tsakanin ma'aurata. 


Binciken mu ya nuna cewa, a matsaƙaita, yawancin mata sun fi son mazansu su ɗauki aƙalla tsakanin mintuna 10 zuwa 15 yayin kwanciyar jima'i, da kuma mintuna 30 idan muka ƙara duka lokacin shiga ciki da kuma lokacin wasanni kafin a tara.


Yayin da wasu mata suka ce sun fi son mazajensu su ɗau aƙalla tsakanin mintuna 20 zuwa 40. Kada ka yi mamaki, saboda wasu ba su yarda ba, sun fi son awa 1 ko fiye. Duk da haka, ba duka mata ba ne, wasu suna da sha’awar jima’i fiye da wasu, wasu kuma sun fi wasu buƙata. Wata mintuna 5 sun gamsar da ita, wasu kuma sai an ɗauki awa ɗaya don gamsar da su.


Abun dubi a nan shi ne, kana buƙatar karantar matarka/mijinki muddin kuna son kiyayewa da rinjaye a cikin wannan harkar. Yana da kyau a lura cewa, yana daga cikin ladubban da ɗa’a na Musulunci, gamsar da abokin tarayya. [Ali bin Abi Talib]


Bayan shawarwari da bincike, na sami damar fitar da wasu hanyoyi da shawarwari don taimaka muku shawo kan wannan matsalar. Da fatan za a yi la’akari da shawarwari masu zuwa:


Kafin Saduwa-:


Ambaton sunan Allah

Abu na farko da ya kamata ku fara shi ne, kiran sunan Allah. Wannan shi ne mafi ƙarancin. Za ka iya karanta addu’ar da Annabi (SAW) ya koyar lokacin kwanciyar aure; “Bismillah, Allahumma jannibnash-shaytan wa jannib-ash-shaytana ma razaƙtana”.


Addu’ar za ta kori kowane ɓangare na Shaiɗan daga mu’amalarku. Wasu cututtukan da suka shafi jima’i galibi ana danganta su da kasancewar shaiɗan da aljanu.


Ƙa’ida ta farko: Kafin ka wadata kanka a gaban matarka, yana da kyau ka sauƙaƙa wa kanka, ma’ana, kayi fitsari. Lokacin da mafitsara ta cika, tana tilasta maka fitar da maniyyi kafin ka shirya.


Tsafta: Ita al’aura ba koyaushe take cikin tsabta ba, don haka a tsaftace ta da ruwa ko kuma yin cikakken wanka kafin kusantar juna. Wannan zai haifar da kwanciyar hankali, lafiya da tsaftataccen yanayi gare ku ku biyu.


Istimna’i ko wasa da al’aura: Wasu masana sun yi bayanin cewa ɗaya daga cikin maganin inzali da wuri shi ne, yin wasa da al’aura kafin saduwa. Wannan na iya faɗuwa ƙarƙashin lokacin wasanni kafin kwanciyar aure.


Kafin shigar, mata za ta iya amfani da hannuwanta, harshenta da bakinta don taimaka muku fitar da maniyyi mai zuwa. A cikin haka, Inzali na gaba zai ɗau lokaci mai tsawo kafin ya ƙara haɗuwa.


Shan magungunan gargajiya: A al’adun Hausawa muna da wata cuta da ake kira “Sanyi”. Abinda ake kira STDs a Turance. Duk da cewa ciwo ne dake rage wa maza da mata yawan sha’awar jima’i, wani lokacin ma yana haifar da bushewar al’aura ko rashin karfin mazakuta. Don haka, akwai magungunan gargajiya da aka fi sani da warkar da irin waɗannan cututtuka. Ko ba ku da lafiya ko kuna da lafiya, ku yi ƙoƙari ku sha waɗannan magunguna, lokaci-lokaci.


Lokacin tarawa(kwanciyar aure)

Yin mu’amalar a hankali da farko – Yin komai cikin harshe yana sa jini yana ƙaruwa, kuma nan da nan, za a aika da sigina zuwa ƙwaƙwalwa, sannan dopamine (sinadari a jikin mutum da ke sanya ambaliyar jin daɗi) ba zai yi jinkirin yin aiki ba.


Lura da iya taku – idan kai mai saurin inzali ne, kiyayewa da iya taku mai kyau zai taimaka maka wajen sarrafa abin, misali, ka san kanka da kyau, ka san yadda da sauri ko kuma a hankali ke saka inzali, don haka ka kiyaye hakan.


Sarrafa numfashi – Haka na nufin numfashin da kake yi shi ma yana tantance saurin fitar maniyyi. Kada ka ba wa kanka wuya, numfashi a sannu-sannu kuma a hankali. Wani lokaci yin numfashi ba tare da kakkautawa ba na iya yaudarar ka wajen yin inzali da wuri.


Hutawa/Sassautawa – idan kun huta, tsokar jikinku ma tana shakatawa tana kasancewa ba a takure ba, haka ma ƙwaƙwalwarku. Sassautawa da yi kamar kuna yin wani nau’i na aiki. Hakan yana kiyaye kwararar jini kuma ana sarrafa shi. Ba za a aika saƙonnin warya zuwa ƙwaƙwalwa don sakin sinadarin ‘dopamine’ ba.


Tazara – Da zarar ka fara jin buƙatar kawowa, ka ɗan dakata ka huta. Kada ka zauna kawai, amma fa ba zama kawai haka ba. A mai da hankali ga wasanni ko wasu abubuwa tsawon mintuna 2 zuwa 4 za ku iya dawowa ku ci gaba.


Canja Salon mu’amalar kwanciyar aure – Babu shakka, wasu salon kwanciyar sun fi wasu kyau idan ana maganar jin daɗin jima’i. Kada ku fara da salon da kuka san zai iya sa ku saurin inzali. Sai dai idan kun ji kun kai wata ƙuloluwar matsayi na jin daɗi, sai ku yi sauri ku canza zuwa wani salon.


Tunaninka kamanninka – Masana ilimin halayyar dan adam sun yi imanin cewa jima’i ba koyaushe yake a kan ɓangarorin al’aura ba. Ƙololuwar jin daɗi ana sarrafa shi ne ya fito daga ƙwaƙwalwa. A lokacin jima’i, mata da miji suna barin tunanin haka ya rinjaye su.


Idan ka cire tunaninka daga gare shi, ka guje wa tarkon da za ka faɗa na sauri sakin sinadarin ‘dopamine’ da wuri. Yayin da ake saduwa, yi ƙoƙari ka karkatar da tunanin zuwa abubuwa, kamar aikinka, kasuwanci, fim, ko wani abu da ke tsoratar da ku; wani abu da zai sa a kore ku daga wurin aikin. A cikin haka, kuna tsawaita sha’awar sakin maniyyi da wuri.


Dabarar kwaroron roba mai kauri – Kororon roba mai kauri yana taimakawa sosai wajen tauye jin daɗin mai yawa. Don haka, yana hana jini dake aika sako zuwa ƙwaƙwalwa. Hakan na iya saku samun tsawaita inzali.


Matse kan alaura – duk lokacin da ka ji ka kusa kawowa, cire alaurarka, sannan ka matse ƙasan kan. Watau, matse ƙasan kan azzakarin na tsawon daƙiƙa 10. Wannan dabarar tana hana kawowa a lokacin.


Kallon Sha’awa ga abokin zama – abu ne na al’ada ga mace da namiji su yi tunanin juna yayin kwanciyar aure. Yawan wannan tunanin na iya motsa dopamine wanda zai sa ku sakinsa da wuri.


Tasirin nishi na mata da numfashi – Shi ma so samu a rage ko a daina don yana da tasiri wajen saurin kawowa.


Bayan Tarawa


Motsa jiki  

Babban maganin matsalar rashin ƙarfin mazakuta da da saurin kawowa, shi ne motsa jiki. Ƙarfafan maza lafiyayyu suna daɗewa a mu’amalar aure fiye da sauran nau’ikan maza. Motsa jiki yana taimaka maka ka ƙona sukari da kitsen da ke zaune a cikin mafitsara kuma yana sa ka so ka saki ‘Dopamine’ da sauri.


Wanke al’aura bayan saduwa 

A duk lokacin da kuka sadu da iyalanku kuka gama, sai ku tsaftace al’aurarku sannan ku ɗaura alwala kafin tafiya zagaye na biyu ko na uku. Yana daga cikin sunnar Annabinmu masoyinmu (S.A.W). Yin jima’i a kai-a kai ba tare da tsaftacewa yana haifar da taɓarɓarewar da rashin ƙarfin mazakuta.


Yin amfani da man ‘Lubricant’ 

Suna da kyau don suna sauƙaƙa mu’amalar aure sannan suna hana yawan amfani da ƙarfi domin yawancinsu suna da sinadarai masu rage yawan kuzari dake hana ka jin matsananciyar sha’awa. Don haka, tasirinsu yana rage saurin inzali. Man Durex Classic ya fi dacewa, saboda ba shi da mai wanda ke da yauƙi da sinadarin hana haihuwa. Ba shi da wata illa.


Shan ruwa da yawa 

Ruwa yana aiki wajen cire ma’anidai masu illa daga jiki. Lokacin da kuke shan isasshen lita na ruwa a rana, yana fitar da duk abubuwan da ba a so a cikin jinin ku, don haka yana haɓaka kuzarinku.


Sanin abincin ku 

Wasu nau’ikan abinci da abubuwan sha da muke ci suna da illa ga rayuwar jima’i. Misali sugar, lemun kwalba masu gas, tarkacen abinci wanda ba su da nau’ikan gina jiki, da dai sauransu. Suna rage sha’awar jima’i kuma suna haifar da rashin kuzari ga namiji.


Yin mu’amala akai-akai (Be Regular) 

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da fitar maniyyi da wuri shine idan aka dau lokaci mai tsawo ba tare da saduwa ba. Yin jima’i a kai-a kai yana taimaka maka ƙarin ƙarfin tsokan wajen da kuma ba ka ƙarfin juriya.


Abunda nake nufi da mu’amala a kai-a kai shi ne, aƙalla sau 5 zuwa 7 a mako. Amma duk da haka, Ali binu Abi Talib ya ce yawan jima’i yana kashe mutum ko kuma ya sa shi saurin tsufa.


Bayani a kan mata Lokacin saduwa:

Har tsawon wane lokaci ne mace ke son namiji ya kasance a yayin kwanciyar aure? Amsar wannan tambayar shi ne, matsakaicin adadin mata sun fi son lokacin jima’i ya kasance akalla mintuna 10 zuwa 15. Wasu sun fi son ya fi haka. Don haka, ku karanci mazajenku yadda kuke koyon dabarun aikinku.


Yaya tsawon lokacin da suke ɗauka kafin su yi inzali? Babu tabbataccen amsa ga wannan tambayar. Ya bambanta daga mace zuwa mace. Amma dabarunku a cikin wasanni kafin saduwa na iya ƙayyade yadda suke saurin inzali ko akasin haka.


Jima’i wasa ne ga mata 

mace ba za ta ji daɗin kusanci ba idan tana bakin ciki ko cikin damuwa. Wannan shine dalilin da ya sa yana da kyau a sa su farin ciki koyaushe kuma a taimaka musu wajen rage damuwa. Damuwa tana sa su daina sha’awar jima’i kuma a wasu lokuta yana shafar al’aurar su ta bushe. Idan tana so, tana jin daɗi, idan ba ta so, za ta ji zafi ne da rashin jin daɗi yayin saduwa.


Shin mata suna yin inzali? Eh wasu matan suna inzali kamar maza, duk ya dogara da abin da kuke musu don tada musu sha’awa da sauri kuma da abunda kuke musu su kai ga ƙololuwar sha’awa da jin daɗi. Idan ka iya da kyau kuma ka san abin da za ka yi don faranta mata rai, tabbas za ta yi inzali.


Me ke sa mata sha’awa? Wannan tambaya ɗaya ce da ta farko, babu amsa takamaimai. Mata kala-kala ne, kuma mata daban-daban suna da wuraren jin daɗi daban-daban. Da fatan Allah ya zaunar da dukkan ma’aurata lafiya a gidajensu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post