Dabaru 8 na samun gamsar da iyali a yayin saduwa |
Wani sakamakon bincike ya gano cewa matsalar rashin haihuwa kan shafi ma’aurata shida a cikin ma’aurata 10 a duniya.
Binciken ya kara da cewa mafi yawan lokuta akan samu magidanta uku daga cikin magidanta shida dake fuskantar matsalar rashin haihuwa.
Likitoci sun yi kira ga ma’aurata da su rika zuwa asibiti don ganin likita a maimakon su zauna a gida ana ta zarge-zarge da ba haka ba.
Jami’an lafiya sun bayyana cewa ana iya magance wannan matsala idan har an gano da wuri.
Dabaru 8 na samun gamsar da iyali a yayin saduwa
Ga jerin wasu hanyoyi 8 na Gamsar Da iyali yayin saduwa
1. Daina Shan giya da taba
Baya ga cutar da lafiyar mutum da shan taba da giya ke yi, wadannan abubuwa na hana namiji haihuwa.
Domin guje wa irin haka ya kamata maza su rage yin ta'ammali da giya da taba ko su daina sha gaba daya.
2. Shan vitamin C
Vitamin C sinadarin ne dake taimakawa wajen warkar da rauni a jikin mutum sannan yana taimakawa wajen warkar da mura.
Vitamin C na hana rashin haihuwa a jikin namiji domin yana inganta karfin maniyyi. Don haka yana da kyau a guji shan vitamin C.
3. Samun hutu
Yawan yin aiki ba tare da samun hutu ba na daga cikin abinda ke haddasa cutar kwakwalwa, sannan da hana namiji iya gamsar da iyalinsa inda haka ke hana namiji iya yi wa mace ciki, idan kana son karin Kuzari da lafiya yana da kyau ka dinga samun hutu.
4. Motsa jiki
Motsa jiki na da mahimmanci ga jikin namiji domin yana taimakawa wajen inganta kuzari a jikin namiji. Yana da muhimmanci ku dinga motsa jiki a kalla sau 3 a duk mako.
5. Kiba
Yawan kiba a jiki na daga cikin matsalolin dake hana namiji iya yi wa mace ciki, Yawan kiba a jiki na hana zuciyar mutum bugawa yadda ya kamata sannan yana rage wa namiji sha’awa. Wannan yasa namiji ba zai iya gamsar da iyalinsa ba.
6. Samun sinadarin Vitamin D
Cin abinci dake dauke da sinadarin Vitamin D na hana namiji samun matsalar haihuwa da rashin gamsar da mace. Nau'in abinci mai dauke da sinadarin Vitamin D sun hada da;
Kifi, hanta, kwai, naman sa na cikin abincin dake dauke da sinadarin Vitamin D.
7. Cin Almonds, hazelnuts da walnuts na kawar da matsalar haihuwa a jikin maza domin suna dauke da sinadarin Vitamin E, zinc, foliat, omega-3 dake inganta kuzarin namiji.
8. Gujewa amfani da magunguna feshi na gonna.
Wasu masana kimiya a kasar Amurka sun gano cewa maganin feshi da ake amfani da shi domin kashe kwari a gonaki na hana maza haihuwa.
A dalilin haka likitoci suka yi kira ga maza musamman manoma da su rika yin la’akari da yadda suke amfani da magungunan feshi a gonakinsu domin guje wa matsalar rashin haihuwa.
Wadannan sune jerin hanyoyi 8 da namiji zai Kauracewa don gudun matsalar rashin haihuwa da kuma rashin gamsar da iyali. Da fatan maza za'a kiyaye da wadannan abubuwan.