Yaya Hukuncin wasa da azzakari har a fitar da maniyyi

Yaya Hukuncin wasa da azzakari har a fitar da maniyyi
Hukuncin wasa da azzakari har a fitar da maniyyi 

Hukuncin wasa da azzakari ko wasa da gaba haramunne kamar yadda alqur'ani da hadisi Ibnu kaseer rahimahullah suka bayyana


Menene hukuncin wanda yake yin wasa da al’aurar sa har ya fitar da maniyyi, musamman a lokacin da yake yin azumi?


Yin wasa da azzakari dab'ia ce da Samari Ke yi don su biyawa kansu bukata ta hanyar fitar da maniyyi. Kuma ba maza ne kadai ke yin wannan dab'ia ta yin wasa da gaba ba, har da mata suma suna yi don fitar da maniyyi. Kuma matasa ne suka fi yin wannan dab'ia ta wasa da gaba. Wannan al'ada itace malamai suke kira da istimna'i, wato mutum yai wasa da gaban sa mace ko namiji har maniyyi yafita.


Hukuncin wasa da azzakari ko wasa da gaba  haramunne kamar yadda alqur'ani da hadisi Ibnu kaseer rahimahullah suka bayyana: Imamu shafi'i da wadanda suka goyi bayansa sun kafa hujja da Haram cin yin wasa da gaba da fadin Allah madaukakin sarki.


والذين هم لفروجهم حافظون إلا على أزواجهم أو ما ملكت أيمانهم) . فإنهم غير ملومين فمن ابتغى وراء ذلك فأولئك هم العادون

Muminai sune wadanda suke kiyaye farjinsu, sai ga matayensu ko kuyanginsu dan basu kiyaye farjinsu akansu ba, su ba'ababen zargi bane, duk wanda yanemi wata hanya bata aure ba kota kuyangarsa wannan mai ketara dokokin Allah ne. Imamu shafi'i acikin littafın Aure yace sai ya kasance Allah ya bayyana kiyaye farjinsu saifa akan matayensu ko abinda damarsu ta mallaka, sai ya zama haramun idan ba matar ka bace ko kuyangarka sai Allah ya karfafı maganar da cewa "wanda ya nemi koma bayan hakan yana cikin masu taka dokokin Allah"


Hukuncin wasa da azzakari

Bisa ga dukkan bayanai daga masana bai halatta namiji yai amfani da azzakari ba sai akan matarsa ko baiwarsa, itama mace bai halarta tai amfani da hannu ta don ta fitar da maniyyi ba, bai halatta jindadi da hannu ba wallahu A'alamu kitabul ummu na imamu shafi'i.


Wasu malaman sun kafa hujja ta haramcin istimna'i wato yin wasa da azzakari ko gaba da fadin Allah madaukakin sarki


وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله سورة النور 33


Wadanda basu samu damar aure ba su kame har sai Allah ya wadata su daga falalarsa. Sukace: umarni da kamewa yana nuna hakuri da rashin samun yin auren ko kuyangar.


A sunnah kuwa sun kafa hujja da hadisin Abdullahi dan mas'ud Yardar Allah ta kara tabbata agareshi yace: Mun kasance tare da Annabi sallallahu Alaihi wasallam muna samari bamu samu komai ba sai Annabi SAW yace damu "ya ku taran samari duk wanda ya samu halin daukar dawainiyar iyali yayi aure, domin ya nesanta kansa daga kamewa daka gani, yana kuma tsare farji, wanda kuma bai samu dama ba to na hore shi dayin azumi domin azumi yana kariya daga fadawa haram. Bukhari 5066.


Daga wannan bayanin za mu fuskanci hukuncin wasa da azzakari, ko yin wasa da gaba ko farji haramunne. Don haka samari da yan mata masu aikata wannan mummunar dab'ia sai su yi gaggawar dainawa, idan kuna da halin yin aure ku yi kokarin yi, idan kuma babu sai ku yi hakuri ko kuma ku dinga yin azumi kamar yadda Annabi SAW ya umarce mu. Domin fitar da maniyyi ba ta hanyar aure ko mafarki ba duk haramunne. Allah ya datar damu amin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post