Yadda ake samun tagwaye |
Sai dai binciken masana lafiya ya gano cewa, haihuwar tagwaye daga macce ce ba daga namiji bane, domin ita ce take daukar juna biyu, kuma ba daga maniyin namiji bane, daga halittar macce ce
Menene alamomin cikin yan biyu, mene yadda ake gane cikin yan biyu, wane irin alamomin ne na yadda ake gane cikin tagwaye?
Wannan duk tambayoyi ne da dubban mutane ke yi tare da neman samun amsa. Mafarkin yan biyu, shine burin kowane ma'aurata. Zai yi wuya ka samu ma'aurata wadanda basa sha'awar samun haihuwar tagwaye. Hakan yasa ake neman dabarun da hanyoyi yadda ake samun tagwaye.
Sai dai binciken masana lafiya ya gano cewa, haihuwar tagwaye daga macce ce ba daga namiji bane, domin ita ce take daukar juna biyu, kuma ba daga maniyin namiji bane, daga halittar macce ce. Mafi yawa akan gado haihuwar tagwaye, wasu kuma ba wani gado haka kawai suke samun wannan Kyautar daga Allah (S.W.T).
A duk lokacin da mace tayi al'ada ta kammala to takan fitar da Kwan halitta. Allah kan halitto mata da wannan kwan da ake kira da (ovum) a cikin mahaifa, ko wace mace da lokacin da take fitarda nata kwan, wata kwana uku kafin al'ada, wata kuma nan take da kammala al'ada take fitar da kwan, wata kuma sai bayan wasu yan kwanaki lokacin ne ake kira da (ovolution period).
A lokacin da take fitar da wannan kwan lokacin ne take saurin daukar ciki ana kiransa da (fertile windows) tana saurin samun juna biyu da zaran an sadu da ita a wannan lokacin. Lokacin ne take fitarda wata majina fara mai haske mai yauki kamar majina wacce ita ce take rike maniyi wato (sperm) a sanda aka sadu da ita, har sperm din ya kai ga tarwatse wannan kwai da ake kira da (ovum) ya zamo saren jini daga nan juna biyu ya shiga.
To a nan, duk sanda mace ta fitarda kwai, guda daya wato (single ovum) to idan aka sadu maniyi ya kai ga wannan kwan zai tarwatse shi su gauraye ya zama saren jini na juna biyu na mace ko namiji amma ba tagwaye ba, dan kwan da ta fitar guda daya ne, idan ko ta fitarda qwai guda biyu (2 ovums) to idan aka sadu da ita maniyin ya kai ga wadannan kwaikwayen guda biyu to zai fashe, sai a samu shigar juna biyu na tagwaye.
Anan,ganyen kubewa na da wasu Sinadirrai na daban masu sa macce ta fitarda qwai ga wacce bata fitarwa da kuma fitarda qwaqwai biyu ga maccen dake fitarwa, waton yana janyo hyperovulation dake kaiwa ga samuwar (two ovums) a lokacin da zata iya daukar ciki.Da zaran an sadu da ita a wannan lokacin to akoi yiwuwar samun juna biyu(samun tagwaye).
Yadda ake samun tagwaye
Haka kuma macen dake da karancin haihuwa ita ma zata iya amfani da wannan ganyen. Za a nemi ganyen ku6ewa mai kyau a wanke a tafasa a zanka miya ko a hada da agushi. za a yi amfani da shi tun kwana uku da fara al'ada har zuwa sati biyu da karewa. a dinga yi akai akai za a yi mamaki.
Shi dai samun tagwaye ba wai maganin bane kamar yadda masana ilimin addini suka bayyana, ba wai shan magani bane ko yin wasu dabaru kamar yadda Wasu ke tunanin hakan ba, shiyasa zakaji ana tamyaba, Yadda ake samun tagwaye, kawai ikon Allah ne idan Yaso ya baku tagwaye ko kuma ya baku daya. Da fatan kun fahimta.