Yadda Ake Saduwa da Mace Mai Ciki

Yadda Ake Saduwa da Mace Mai Ciki
Yadda Ake Saduwa da Mace Mai Ciki 


Masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga saduwa da mace mai ciki, ta hanyar hawa kanta, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe


Da yawa daga cikin ma'aurata basu san cewa suna iya yin jimai ba. Koda yake an samu banbancin ra'ayoyi daga masana da yawa wanda suka yi bayani kan amfanin saduwa da mace mai ciki da kuma illar yin hakan musamman ga lafiyar macen. Wasu kuma masana sun fi karkata kan alfanun da ake samu idan ana jima'i da mai ciki musamman ga ita macen. 


Malam na kan ji wasu mutane na bayyana cewa ba ya halatta idan matar mutum tana da juna biyu ya yi jima'i da ita har sai bayan ta haihu, shin mene gaskiya wannan maganar? 


Mafi ingancin bayani daga masana musamman masana ilimin addinin Islama, sun ce ya halatta a sadu da mace mai ciki a lokacin da take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi da yake cewa: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud: ayim yana cewa :"Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa" Tahzibussunan 193. 


Masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga saduwa da mace mai ciki, ta hanyar hawa kanta, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da abinda ke cikinta. Sannan yawanci mata ba su cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a karanta saduwa a wadannan lokutan. Allah ne ma fi sani


Kenan wannan bayani na likitoci da malaman addinin Islama suka yi, yana nuna cewa babu laifi yin saduwa da mace mai ciki, don yin hakan ma kamar karin lafiya ne a gareta. Sai dai a kiyaye da shawarar da masana suka bayyana cewa Kada a hau kan ruwan cikinta don gudun samun matsala. Yana da kyau a yi amfani da wasu hanyoyi na dabara don saduwa da mace mai ciki.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post