Tarihin Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Tarihin Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa

Tarihin Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa
Tarihin Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa


Cikakken sunan sa shi ne Muhammadu Rumfa ɗan Yaƙubi, sunan mahaifiyarsa Faɗimatu, ance ita mutuniyar ƙasar Rano ce.


Muhammadu Rumfa nagartaccen mutum ne, adali, malami, wanda ba za a samu wani tamkarsa ba a cikin sha’anin mulkin Kano. Ya mulki Kano daga wuraren 1463 zuwa 1499, wato a Æ™arni na goma sha biyar.


A cikin zamaninsa sharifai suka zo Kano, watau su Muhammad Abdulkarim Al Maghili ko Abdurrahmani tare da jama’arsu.


An ce shi Shehu Al Maghili, Annabi Muhammad (SAWW) ne yazo masa a cikin barci, ya ce masa “Tashi ka tafi wajan yamma ka Æ™arfafa Musulunci”. Da ya tashi daga bacci sai ya É—ebi Æ™urar Madina ya zuba a sanho ya zo da ita Æ™asar Hausa. Kowane gari ya shiga sai ya É—ebi Æ™urarsa ya gauraya ta da ta Madina, sai ya ga ba su haÉ—u ba, sai ya wuce. Haka ya rinÆ™a yi har yazo kano, ya É—ebi Æ™urarta ya gaurayata, sai yaga ta zamo abu É—aya, sai yace “Wannan gari shi ne na gani cikin barcina” (amma akwai bambace-bambance masana tarihi akan haka wasu sunce daga kasar Aljeriya ta tafi kano)


Al Maghili ya zauna a wani gari da ake kira Fanisau, wanda yake daf da kano, sannan ya aikewa sarkin Kano Muhammadu Rumfa buÆ™atarsa ta shiga birni. Sarki Rumfa ya tafi izuwa gareshi tare da jama’arsa irinsu Hantari, da Gemun dodo, da Gadangami, da Alfagi, da sauransu, ya taho dashi cikin birnin kano.


Al-Maghili ya zauna a kano ya Æ™arfafa Musulunci cikin wannan gari. Shi ne yazo da littattafai masu yawa ya umarci Rumfa ya gina masallacin Juma'a. Da nan addini ya kara zauna daram a Kano, sai ya wallafa wani littafi mai suna ‘Taj al-din fi ma yajib ‘ala I-muluk’ wanda zai taimakawa Sarki Rumfa gudanar da sha’anin mulki bisa tafarkin Islama daga nan ya yi Æ™aura zuwa Misira tare da barin Na’ibinsa mai suna Sidi Fari a Kano yana cigaba da karatar da mutane addini.


An ce Sarkin Kano Rumfa ya nemi Shehu Al Maghili yayi masa adduoi guda tara waɗanda ana ganin har yau suna da tasiri a Kano. Daga cikin adduoin; an roƙa masa cewa duk wanda yazo Kano har kuma ya samu arziki a Kano, to ya zauna a Kano ba tare da ya koma garinsu ba


Sannan an roÆ™a masa cewa duk cikar da garin Kano zai yi kada a sami yunwa. Wata addu’ar da aka yi masa itace duk wanda ya zo Kano dare ko rana to ya sami abincin da zai ci. Sarkin Kano Rumfa shi ne ya fara abu goma sha biyu a Æ™asar Kano. (Madogara littafin Kano ta Dabo tunbin Giwa).


Shi ne ya gina gidan sarautar kano da har yau ake kiransa da suna GIDAN RUMFA.


Da shekara ta zagayo kuma ya faÉ—aÉ—a ganuwar birni tun daga Æ™ofar dagaci zuwa Æ™ofar Mata, zuwa Æ™ofar gyarta-wasa, zuwa Æ™ofar Æ™awaye, zuwa Æ™ofar Na’isa, zuwa Æ™ofar kansakali.


Da wata shekarar ta sake zagayowa sai ya tare a sabon gidansa.


Haka kuma shine ya kafa kasuwar kurmi, shi ne ya fara dawakin zage domin yaƙi da Katsina.


Shi ne sarki na farko wanda ya fara kulle. Shi ne ya fara Tara-Ta-Kano da kakaki da figini da takalmin jimina. 


Shi ne wanda ya fara baiwa Babanni sarauta; na farkon su ÆŠan kusubi, da ÆŠan jigawa, da ÆŠan turbuna, da sarkin Gabas da sarkin Tudu da sarkun Ruwa da Ma'aji da sarkin Bai da sarkin Æ™ofa. Har gobe ana ambatar duk wanda za a naÉ—a sarkin kano da suna ‘Magajin Rumfa’.


A zamaninsa ƙasar kano ta yi yaki da ƙasar Katsina, wanda sai da aka shekara goma sha ɗaya ana fafatawa a tsakaninsu ba tare da ɗaya ta rinjayi ɗaya ba.


Sarki Muhammadu Rumfa ya sarauci Kano tsawon shekaru talatin da bakwai.


Ana masa kirari da ‘Balaraben sarki ya gyara Æ™asa!’


Allah ya jikan maza. Babban malami kuma inginiyar gini. Shi ya zana kuma ya gina gidan Rumfa a Kano wato gidan sarkin Kano na yanzu wanda hata turawan Engila sunji mamakin wannan tsarin gidan da fadin sa da kuma kwarewa wajen daidaita lissafin ginin. Rumfa ya gaji wannan fasaha da basira wajen kakanin Hausawa da suka fito daka daular Kusch bayan rushewar misran fir'auna.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel