Tarihi Da Kuma Asalin Tashe A Kasar Hausa |
Tashe al’ada ce da akan yi a cikin watan nan mai alfarma, wato watan Ramadan.
Ma’anar Tashe
Masana daban-daban sun bayar da ma’anar tashe bisa yadda suka fahimce shi kamar haka:
Umar (1981) ya bayyana ma’anar tashe da cewa, al’ada ce da akan yi a cikin watan nan mai alfarma, wato watan Ramadan.
C.S.N.L.(2006:431) sun bayyana tashe da wasannin ban-dariya da yara da samari da ‘yan mata ke yi bayan watan azumi ya kwana goma domin samun sadaka.
Yahaya (1978) cewa ya yi, tashe yana daya daga cikin wasanni iri-iri da yara suke shiryawa a watan azumi bayan an sha ruwa, suna bi gida-gida suna yi, manya suna kallo ana raha.
Alhamdu (1973) ya nuna tashe da cewa, yana daga cikin al’adu da dama da Hausawa sukan yi saboda samun shakatawa bayan an sha ruwa idan watan Ramalana ya kama da kwana goma.
A dunkule, tashe wata al’ada ce ta Hausawa wadda ta samu bayan Musulunci wadda yara (maza da mata) da manya maza suke aiwatar da ita a yayin da watan Ramalana ya kai kwana goma.
Asalin Tashe
Tashe ya samo asali ne daga yadda wasu mutane suka dora wa kansu tashin jama’a domin yin sahur. Kasancewar bacci abu ne mai nauyin gaske, sai aka sami wadansu mutane wadanda aikinsu ne su tashi mutane can cikin dare domin su shirya abin da za su ci. Almajirai daga cikin wadannan, sukan tayar da mutane ne ta hanyar yin bara da murya mai karfi. A sakamakon haka, sukan sami sadakar abinci (Umar,1981:4).
Makada da maroka kuma suna tayar da mutane ne ta hanyar kade-kade da wake-wake, sannan bayan azumi sai su bi gida-gida ana ba su abin da ya sawwaka. Akan sami samari majiya karfi da sukan tashi don jin dadi da nishadi suna ‘yan wake-wake don tayar da jama’a.
Kasancewar yara kanana, musamman ‘yan mata, ba su da damar tashi cikin dare, sai suka shiga wasanni suna kwaikwayon abubuwan da ake yi, bayan an sha ruwa. Da haka, sai aka dinga kiran su wasannin tashe.
Da tafiya ta yi nisa, sai ya zamana ba kananan yara kadai suke yin wasannin tashe ba, har da manyan samari wadanda kan yi kungiyoyi suna bi unguwa-unguwa (Umar,1981:5).
Karaye (1970:2) ya nuna cewa, tashe abu ne mai tsohon tarihi wanda aka fara shi tun lokacin Sarkin Kano Bello (1882-1893). Ya ci gaba da cewa, tashe ya fara ne da siffar roko, inda maroka sukan bi gidajen manyan mutane da dandali-dandali suna yi domin su yi samu.
Misali, ya nuna cewa, tasussukan da suka fi tsufa su ne; tashen Baza da tashen Zakari Mai Lela da kuma tashen Nalako.
Alhamdu (1973:3) ya bayyana cewa, tashe al’ada ce ta Musulmi, kuma a ko’ina a kasar Hausa ana yin ta, kuma ta samo asali ne daga addinin musulunci, kuma yadda ake gabatar da shi, ya bambanta daga guri zuwa guri.
Jerin Tashe Da Ake Aiwatarwa A Kasar Hausa
Tashen Nalako
Tashen macukule
Tashen Ka yi rawa kai malam ka yi rawa
Tashen Jatau mai magani
Tashen Mai kiriniya
Tashen dan dukununu
Tashen Zuciyar mai tsumma
Tashen Ga Mairama ga Daudu
Tashen Auren gidan Sharu ya kare
Tashen mai ciki
Tashen Iya duba-duba
Tashen Tagajera
Tashen A sha ruwa
Tashen Tsoho da gemu
Tashen ‘Yar gajera
Tashen Iya talgenki zai zube
Tashen Baba da satar bulo
Tashen Malami da Karuwa
Tashen Danda
Tashen Namadi
Tashen Birin Kano
Tashen Mai kwadayi
Tashen mai idon sakaina
Tashen Alhaji ba ni kudin zancena
Tashen Iya ga barawon ice
Tashen wayyo za na haife Abdulkadir
Tashen dalibar makarantar boko ta yi ciki
Tashen kar ka tashi Wali
Tashen Karuwa ta yi arziki za ta gida
Tashen ‘Yanmata a daina bilicin
Tashen ragadada
Tashen danbera mai shiga rami
Tashen student ta rasa aikin yi
Tashen ko da dan hatsi ga zabo zai mutu
Tashen dantsoho ga mutuwa nan
Amma tashe Yana canjawa da salo saboda Wani zuwan Babban Wani Abu Da Ya Faru. Kamar:
Tashen Karyar Dimka Ta Kare, Gashi A Hannun Soja (1976) Dimka Dai Shine Sojan Ya Shirya Juyin Mulki Da Aka Kashe Janar Murtala, kana Ya Gudu, Daga Baya Aka Kamo Shi.
Madogara
Alhamdu, I.D.(1973) Tashe Musamman na kasar Kano, Report on Summer
Project, Kano: ABC,ABU.
Bargery, G.P.(1934) Hausa-English Dictionary and English-Hausa vocabulary,
London: Odford University Press.
Buhari, M.(1988) “Nazarin Jigon Wasu kagaggun Labarai na Hausa” Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Chamo, I.Y. (2006) Sako a Finafinan Hausa:Nazari a kan Jigo da Rabe-rabensa.
Kundin Digiri na Biyu, Kano: Jami’ar Bayero.
dangambo,A.(1981) “daurayar Gadon Fede Waka” Kano: Sashen Koyar da
Harasunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
dangambo, A.(1982) “Jigon Bandariya a Adabin Hausa” Departmental Seminar.
Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
dangambo, A.(1982) “Jigon Bandariya a Adabin Hausa” Departmental Seminar.
Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
dangambo, Halima,A.(2002) “Salon Sarrafa Jigo a Adabin Baka na Hausa: Nazari
Kan Jigon Fadakarwa, Kundin Digiri na daya, Kano: Jami’ar Bayero.
East,R.M. da Wasu (1948) Zaman Mutum da Sana’arsa, Zariya: NNPC
Gusau, S.M.(1983) “Wakokin Noma na Baka: Yanaye-yanayensu da Sigoginsa” a
cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, Vol.1 No.1
Kano: Bayero University.
karaye, M. (1970) Tashe By Male People, Report on Summer Project, Kano:
ABC,ABU.
Mukhtar,I (2002) Jagoran Nazarin kagaggun Labarai, Kano: Joji Publishers
Umar, M.B.(1981) Wasannin Tashe, Zaria: NNPC
Yahaya, I.Y (1978) “Nazari Kan Yanayin Wasan Kwaikwayo na Hausa, Takardar
da ya gabatar a taro kan Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar bayero.
‘Yar’aduwa, T.M.(2001) “Wasan Kwaikwayo: Sigoginsa da Jigoginsa” a cikin
Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies Vol.1. No.1. Kano: Bayero University.