Shin yin wasa da al’aura na iya haifar da kankancewar azzakari?

Shin yin wasa da al’aura na iya haifar da kankancewar azzakari?
Shin yin wasa da al’aura na iya haifar da kankancewar azzakari?


Matakin farko na magance kankancewar gaba shine gane cewa kana da shi. Rashin ƙarfin azzakari ko rashin Kuzari yayin jima’i yana nuna rashin karfin gaba.


Istimna'i ko yin wasa da gaba wanda a turance ake kira da masturbation, yanayi ne na jima’i na ɗan adam ta hanyar yin wasa da gabansu don su biyawa kansu bukatar sha'awa. Wannan dab'ia ta istimna'i mata da maza duk suna yi. Dab'ia ce da ta zama ruwan dare a tsakanin matasa. A gefe guda, wasu na  tambaya shin ko yin wasa da gabansu zai iya haifar da matsalolin ƙarfin azzakari ga maza? A cikin wannan topic, za mu bayyana muku alaƙar istimna'i da matsalar kankancewar gaba ga maza.


Matakin farko na magance kankancewar gaba shine gane cewa kana da shi. Rashin ƙarfin azzakari ko rashin Kuzari yayin jima’i yana nuna rashin karfin gaba. Zai iya faruwa ga kowa a kowane lokaci, amma maza masu shekaru sama da 40 sun fi fuskantar haɗarin kamuwa da rashin karfin gaba. Matsalolin jiki kamar ciwon sukari, cututtukan zuciya, da kiba, da kuma matsalolin kiwon lafiya na kwakwalwa kamar damuwa, da baƙin ciki, duk an danganta su da haifar da rashin ƙarfin azzakari.


Shin yin wasa da al’aura na iya haifar da kankancewar azzakari?

WebMD kungiyar masu bincike kan harkar lafiyar dan adam sun bayyana cewa babu wata shaida da ke nuna cewa wasa da al’aura, ko wasa da gaba ko istimna'i yana haifar da rashin ƙarfin azzakari. Sun ma bayyana cewa yin wasa da azzakari na rage barazanar rashin karfin gaba ga maza. Binciken da aka buga a cikin Jaridar Kimiyyar Jima’i ya nuna cewa wasa da gaba yana rage yawan rashin ƙarfin azzakari a maza, wanda hakan zai iya kasancewa saboda yawan gudanar jini a yayin wasa da azzakari.


A cewar healthline, yin wasa da gaba mai yawa, a gefe guda, na iya haifar da alamun cututtukan kwakwalwa wanda, a bi da bi, zai iya taimakawa wajen haifar da rashin karfin azzakari. Don haka dai yawan yin istimna'i ko wasa da gaba na iya haddasa kankancewar azzakari da lalalata tunani.


Idan Kana daga cikin wadanda kept aikata dabiar istimna'i ko wasa da azzakari ku yi gaggawar dainawa, ku samu ku yi aure don kare Kanku daga aikata zinar hannu. Fatan masu aikata istimna'i za su yi kokarin dainawa don kare kansu daga kankancewar azzakari.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post