Wasa Da Al’aura |
Wasa da gaba ko wasa da farji da wasa da azzakari yanayi ne da mutum ko dai mace ko namiji matasa ko masu shekaru ke kebewa inda babu wanda zai gansu don su yi wasa da alaura su biyawa kansu bukata
Wasa da gaba ko wasa da al’aura, wanda galibi ake cece-Kuce na rashin fahimta akan lamarin, wani yanayi ne na al’ada da ake kallon sa a matsayin jima’i na ɗan adam. Ba ya haifar da makanta, rashin ƙwaƙwalwa, ko wasu illolin lafiya marasa kyau kamar yadda Wasu ke fadi. A cikin wannan topic na yau, za mu kawo muku maganganu na masana kan yin wasa da al’aura, don haskakawa masu yin wannan dabia.
Fahimtar wasa da gaba (Al’aura)
Wasa da gaba ko wasa da farji da wasa da azzakari yanayi ne da mutum ko dai mace ko namiji matasa ko masu shekaru ke kebewa inda babu wanda zai gansu don su yi wasa da alaura su biyawa kansu bukata. Wannan dabia ta wasa da gaba masu aure suna yi da wadanda basuda aure. Sai dai bincike ya gano kaso 80 cikin 100 na wadanda ke yin wasa da al’aura matasa ne da ba su da aure. Don jin sahihin bayani bari mu kawo muku maganganu kan illar yin wasa da alaura.
Yin wasa da Al’aura Yana Haifar da Makanta da Rashin Ƙwaƙwalwa; A akasin abinda aka yarda da shi, babu wata hujja ta kimiyya da ke danganta yin wasa da al’aura na jawo makanta ko rashin ƙwaƙwalwa. Wadannan kamar tatsuniyoyi marasa tushe da asali ne cewa yin wasa da gaba na haifar da sakamako mara kyau ga lafiya. A zahiri, wasa da al’aura hanya ce mai aminci kuma lafiyayya dake sa jikin mutum yai lafiya da kuma jin daɗin jima’i. Babu wani binciken kimiyya da ya nuna aikata hakan na sa mutum ya makance
Yin wasa da Al’aura Yana Haifar da Matsalar Rashin Ƙarfin Azzakari; Wasu mutane suna damuwa cewa yawan yin wasa da al’aura zai iya haifar da matsalar rashin ƙarfin azzakari. Duk da haka, wasa da al’aura wani ɓangare ne na al’ada ga wasu mutanen kuma ba ya haifar da rashin karfin azzakari. Idan Kana tunanin wasa da gaba ne ke haddasa maka rashin karfin azzakari, ya kamata ku tuntuɓi likita, saboda wasa da al’aura ba shi da alaƙa da haddasa rashin karfin gaba.
Yin wasa da Al’aura Yana jawo rashin Haihuwa; Wata tatsuniyar da aka saba yi ita ce yin istimna'i ko wasa da gaba zai iya shafar kwayoyin haihuwa. A gaskiya, tsarin haihuwa na maza da mata ya bambanta da jin daɗin jima’i da ake samu yayin wasa da al’aura. Yin wasa da farji ko wasa da azzakari ba ya shafar ikon mutum na haihuwa.
Karin bayani game da wasa da Al'aura; Bayanai da dama na nuni da cewa yin wasa da gaba yana iya haddasa hadari ga lafiyar mai yi, yana lalata al'aura musamman mata dake amfani da vibrator(azzakarin roba) yana haddasa cuta a farji, sannan yana lalata aure musamman idan miji ko mata ya fuskanci abokin zamansa yana aikata hakan, sannan yana haifar da cutar kwakwalwa. Duk wannan tatsuniyoyi ne a cewar binciken kimiyya.
Amfanin yin wasa da al’aura
Karin bayani game da masu fadar maganganu marasa tushe kan yin istimna'i, yana da mahimmanci ku san wasu daga cikin amfanin wasa da gaba. A cewar Jenni Skyler wani masanin Jima'i, yin wasa da al’aura yana karfafa garkuwar jiki da inganta lafiyar jiki. Wasu daga cikin amfanin sun hada da;
1. Rage Damuwa: wasa da azzakari ko wasa da farji har a samu biyan bukata yana rage damuwa da samar da gamsuwa.
2. Bacci Mai-dadi: koda yaushe jiki zai samu gamsuwa da nustuwa da taimakawa yin bacci mai dadi da nagarta
3. Rage Radadi: musamman ga mata yin wasa da farji zai taimaka musu rage zafi da radadin ciwon mara da sauran ciwon jiki.
4. Kulawa Da Kai: yin wasa da al’aura kan iya taimakawa mutum ya zama Jikinsa yai kyau,
Daga Karshe
Tatsuniyoyi game da cewa yin wasa da al’aura kan iya haifar da makanta, rashin kwakwalwa, ko dukkan wasu cutuka da babu tushe a kimiyya. Wasa da al’aura babu wata matsala shima kamar jimai ne da za'a yi tsakanin mace da namiji. Wannan dai bincike ne mara tushe da sukai wannan bayani game da yin wasa da al’aura.
Sai dai mu munsan hakan a addini haramunne kuma yana da illoli sosai ga lafiya. Don haka kada ku yi amfani da wannan binciken ku dinga aikata wannan mummunar dabia, don tana da illa sosai ga lafiyar dan adam mace da namiji. Da fatan Allah ya ganar damu yasa mu kiyaye.