Hukuncin maziyyi ga mai azumi |
Hukuncin sa ga mai azumi Malamai sun samu sabani akan, shin Maziyyi yana karya azumi ko baya karyawa
Shin fitar maziyyi ga mai azumi yana karya azumin kamar yadda fitar maniyyi ke lalalata azumi? Wannan itace tambayar da muka samu daga wajen mabiyan mu.
Wannan dalilin ne yasa muka zurfafa bincike kan lamarin, duba da ganin zuwan watan Azumin Ramadan, wanda a cikinsa ne Allah S.W.T ya haramtawa Musulmi yin abubuwan alfasha wanda kan iya lalata azumin.
Hukuncin maziyyi ga mai azumi
Kafin mu yi bayani kan hukuncin fitar da maziyyi ga mai azumi da farko za mu fara yin bayani kan Menene Maziyyi? Iman Nawawi acikin Littafinsa mai suna Al'majmu'u yana cewa maziyyi wani Ruwa ne Fari mai fatsi- fatsi, wato marar kauri yana fita ne yayin sha'awa karama, ba'a jin dadi lokacin fitarsa kuma baya tunkudar juna a lokacin fitar sa, mafi yawan lokuta ba'a sanin fitar sa.
Fitar da maziyyi maza nayi, mata suma suna fitar dashi, amma mata sunfi maza yawan fitar wa fiye da maza. Amma wani binciken likitoci ya bayyana cewa akwai wasu mazan da basa fitar da maziyyi gabaki daya, wasu kuma suna fitar dashi ne bayan fitar maniyyi.
Yaya Hukuncin maziyyi ga mai azumi?
Hukuncin sa ga mai azumi Malamai sun samu sabani akan, shin Maziyyi yana karya azumi ko baya karyawa Amma magana mafi inganci baya karya azumi, ya kasance maziyyi ya fita ne saboda kallon mace ko Kiss ko romance duka baya karya azumi.
Wannan shine Ra'ayin da mazhabar; ~Abu Hanifa R.A ~Iman Shafi'l R.A ~Imam Ahmad R.A acikin wata ruwayarsa, kuma Ibn Taimiya ya rinjayar da wannan ra'ayi na Iman Ahmad.
Amma mu Malikawa wato Malikiyya Sun tafı akan fitar Maziyyi yana karya azumi musamman ma in mutum ne ya jawo shi da Gangan to yakan karya mishi azumi kuma sai ya rama azumin.
Ibn Usaimeen yana cewa acikin Littafin sa na "Sharhul Mamta'un" Yana cewa Magana mafi inganci kuma wanda itace daidai shine maziyyi baya karya azumi, kuma wanda yayi maziyyi a lokacin azumi azumin sa bai baci ba.
Ibn Baz yake cewa: "Fitar maziyyi ga mai azumi baya karya azumi wannan shine zance mai inganci a wajan malamai magabata.
Fatawa ibn Baz Daga bayanan da suka gabata na nuna magana mafi inganci a wajan Malamai magabata shine Maziyyi baya karya azumi, domin babu wani Nassi wanda ya nuna cewar Maziyyi yana bata azumi. Allah ne Mafi Sani.