Shin ƙasar Misira a nahiyar Afirka take ko Yankin Gabas ta Tsakiya? |
Misira dai ta kasance ƙasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin ƙasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin al'ƙahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka tun ƙarnoni da dama da suka gabata.
Taƙƙaitaccen bayanin alaƙar ƙasar Misira da nahiyar Afirka a hannu ɗaya, da kuma Yankin Gabas ta Tsakiya a ɗaya hannun.
Tun asalin tarihi kawo yau, ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewarta akan marararraba. Ga ta kusa da nahiyar Turai, sannan kuma ga ta a matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma ita ce ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar bahar Maliya.
Misira dai ta kasance ƙasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin ƙasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin al'ƙahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka tun ƙarnoni da dama da suka gabata. Sannan kuma har ila yau ga ta a ƙarshen kogin nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. Saboda haka idan aka yi la'akari da waɗannan dalilai na tarihi, to za a iya fahimtar dalilin da ya sa matsayin ƙasar Misra yake da 'yar rikitarwa.
Suma kansu Misirawan a tsakanin su, sukan kasance cikin ruɗani a game da batun nahiyar da ya kamata su yi tutiya da ita a matsayin nahiyarsu. Ga su dai a cikin kwazazzabon nilu, da mediterenean, da Sahara, har ila yau kuma ga su cikin duniyar Musulmai, duk kan waɗannan siffofi, siffofi ne da ba kasafai ya kamata a ce wata ƙasa guda ɗaya ta haɗa su ba. To sai dai duk da haka za a iya cewa, mafi yawan faɗin ƙasar yana ɓangaren nahiyar Afirka ne. To amma fa duk da haka ana kallon garuruwan da suke lardin sinai na ƙasar Misiran a matsayin ɓangaren nahiyar Asiya, kasancewar su, suna yankin gabashin ƙasar ne.
A zamanin da can, dangantakar Misra da ƙasashen da ke Afirka na da matukar ƙarfi. To amma tun lokacin da Siriyawa da ke ƙarƙashin daular Rumawa suka mamaye Misira, a ƙarni na bakwai kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam, sai Misira ta karkata zuwa ga Yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar harkokin al'adunta da na addininta da na siyasarta da kuma na tattalin arzikinta. Kuma mafiya yawan Misirawa suna danganta kansu ne da Larabawa kuma 'yan Yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau kuma wasu dayawa daga cikinsu, kusan ace waɗanda suke su ne 'yan asalin ƙasar ta Misira, waɗan kuma aka fi sani da Nubiyawa, suna danganta kansu ne da Afirka. Hasalima suna iƙirarin su jinin Afirka ne.
Babu shakka dai idan aka bi salsala ta tarihi, shekaru 200 da suka gabata, Misra tana da alaƙa mai ƙarfi da ƙasashe irin su Sudan da Habasha da Libya da ma wasu ƙasashe da dama na nahiyar Afirka. Kuma ba tare da wani kokwanto ba, Misra za ta ci gaba da cin tudu biyu, a matsayinta na ruwa-biyu, wato ga ta dai 'yar Afirka, kuma 'yar Yankin Gabas ta Tsakiya.