Menene Hukuncin maziyyi A tufafi

 Menene Hukuncin maziyyi A tufafi


Hukuncin maziyyi a tufafi, shi dai maziyyi najasa ne, ba kamar maniyyi wanda malamai suka yi saɓani akan shi ba, kuma sahihiyar magana a wurinsu a kansa ita ce: Shi (maniyyi) ba najasa ba ne. (Fiqhus Sunnah)

 

Wasu na tunanin cewa idan maziyyi ya fito musu a tufafi babu wani hukunci, zasu iya yin ibada a haka. Sai dai wannan tunanin ba daidai bane, kowane abu yana da irin nasa hukuncin. Hukuncin maziyyi a tufafi shima yana da nasa sharuddan da abubuwan da ya dace ayi. 


Da farko idan ban da fitsari akwai abubuwa guda uku da suke fitowa daga mafitan fitsarin, su ne: Wadiyyi da Maziyyi da Maniyyi. (Ibn Abi-Shaibah: 1/89). 


Hukuncin maziyyi A tufafi

Shi dai maziyyi ruwa ne tsararo mai yauƙi da yakan fito saboda ƙaramar sha’awa, ba da tunkuɗar juna ba, kuma ba tare da samun sakin gaɓoɓin jiki a bayan fitowansa irin na maniyyi ba. Wani lokaci ma ba a sanin fitowarsa.


Hukuncin maziyyi a tufafi, shi dai maziyyi najasa ne, ba kamar maniyyi wanda malamai suka yi saɓani akan shi ba, kuma sahihiyar magana a wurinsu a kansa ita ce: Shi (maniyyi) ba najasa ba ne. _(Fiqhus Sunnah)_ 

 

Munsan cewa duk abinda yake najasa ne, ai dole ne ai tsarki a kansa musamman idan ya taba tufafi. Maziyyi ana samunsa ne yawanci ta hanyoyin da suke motsar da sha’awa, kamar haka:


Abubuwan Da Ke Jawo Fitar Ruwan Maziyyi 

1. Yin tunani a kan al’amarin saduwa a tsakanin masoya. Ko miji da mata 

2. Kallon sha’awa ga jiki ko al’aurori a tsakanin masoya.

3. Sauraron maganganun sha’awa a tsakanin masoya.

4. Murmushi ko dariyar sha’awa a tsakanin masoya.

5. Magana ko hirar sha’awa a tsakanin masoya.

6. Keɓantuwa a wani wurin tsakanin masoya.

7. Sansanan ƙamshin juna a tsakanin masoya.

8. Shafar wani sashe ko dukkan jiki a tsakanin masoya.

9. Haɗuwar al’aurorin masoya ba tare da zarcewa ko nutsewa ba. _(Sabon Saurayi)_ 


Hukuncin maziyyi a tufafi, shine wajibi ne ga wanda maziyyin ya same shi ya wanke dukkan al’aurarsa gaba ɗaya (azzakarinsa da marenansa), kuma ya wanke tufafinsa inda maziyyi ya taba, sai ya sake alwala. _(Al-Bukhaariy: 269, Muslim: 303, Abu-Daawud: 208)_ 


Idan kuma maziyyin ya shafi tufa ne, to shari’a ta yi sassauci in aka ɗebi ruwa aka jiƙa wurin da ya shafan kawai, ya yi. Kamar dai fitsarin jariri. _(Abu-Daawud: 210, At-Tirmiziy: 115, kuma ya ce: Kyakkyawa ne, ingantacce)._ 


Daga wannan bayanai za mu iya gane cewa shikakai maziyyi ai najasa ne, kuma hukuncin maziyyi a tufafi shine mutum ya wanke tufafinsa. Da fatan Allah ya kara ganar damu addini da kiyayewa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post