Kabilu Biyar Mafiya Tsadar Aure A Nijeriya |
Kowane bangare a Nigeria da irin salon Yadda suke gudanar da neman aure da bikin aure. Sannan kuma kowane akwai yanayin kashe kudin su
Shin ko kunsan adadin kabilu a Nigeria mafiya tsadar aure? Idan baku sani ba ga su na tattaro muku su a takaice don ku San su.
1. Shuwa Arab (Jihohin Borno da Yobe)
Bukukuwan aure na wannan kabila suna da yawa akan yi kwana bakwai ko fiye da haka ana shagulgula. Ango zai bada sulan zinari 12 da kuma Shanu 15 zuwa 100, sai dai yawan Shanu na iya karuwa musamman ma idan matar tana da kyau sosai ko ta na da ilimin zamani.
2. Bororo (Jihar Adamawa)
Wanda zai auri ‘yar kabilar Bororo shi Angon sai ya ba mahaifan wadda zai aura Shanu daga 10 zuwa15 wannan yana nufin milyoyin Nairori ke nan, bayan kuma akwai abubuwan da za a bukata ya bada.
3. Kalabari (Jihar Ribas)
An san ‘yan Kabilar Kalabari da sa kudin auren ‘yarsu da yawa da abubuwan da za a saya fiye da kowace kabila a Nijeriya. Ango ana sa shi ya ba da kudade daban- daban saboda yin bikin auren. Sadakin auren ‘yar kabilar Kalabari yana iya kai wa Naira miliyan daya ko fiye da haka.
4. Okrika (Jhar Ribas)
Angon ko wanda yake son auren ‘yar kabilar Okrika sai ya yi kasafin akalla Naira 400,000 da zai ba mahaifin yarinyar yayin da ita kuma mahaifiyar zai ba da daga Naira 250,000 zuwa 300,000 hakan ya sa jimillar kudaden sun kai Naira 700,000. Wannan duk ba wani abu ba ne domin kuwa da akwai sauran iyalai kamar yara mata marasa aure, kawayen amarya da suke tsararraki, Kakanni, kannen uba, da kuma ‘yan’uwan mahaifiyar amarya da za a yi musu hidima. Al’amarin auren ‘yar kabilar Okrika wato sadakin ko kudin aure abin na iya kai wa Naira milyan daya da rabi ko fiye da haka.
5. Ibo (Inyamuari)
A sashen Ibo an fi yin auren gargajiya, al’ummar wurin sun fi shirya wa irin hakan, shi ya sa zai yi wuya ga mahaifan Amarya su rage kudin da ake biya don kawai su saukaka wa surikinsu. Kayan da za a saya sun bambanta ne daga gari zuwa gari ko unguwa zuwa wata unguwa sai dai akwai wadansu abubuwan da ba a canza su. Wani lokaci shi surukin da za yi aure yana taimakawa wajen ayyukan da ake yi a garin da zai yi aure, wannan kuma ya danganta ne da irin aikin da za a yi. A wasu wurare farashin yakan bambanta ne saboda wasu abubuwa, kamar matakin ilmin ita Amaryar, irin abin da ta karanta, da dai sauran wasu abubuwa. Saboda hidindimun da ake yi a auren Ibo, da wahala a iya iyakance abin da za a kashe.