Idan Mace Tana Son Ka, Za Ta Fara Yi Maka Wadannan Abubuwan

Idan Mace Tana Son Ka, Za Ta Fara Yi Maka Wadannan Abubuwan
Alamomin da budurwa ke nuna tana son namiji 


Idan budurwa ta kamu da son saurayi akwai wasu Alamomin da take nuna masa don ya ankare da bukatar ta 

Budurwa idan tana son namiji za ta fara nuna masa wasu alamomi don yai mata magana. Wadannan saƙonnin alamomin suna bambanta a cikin yadda ake nuna su, amma za ka iya gano su idan ka kula. Wannan ne wasu daga cikin alamomin da suke fitowa kamar haka:


Alamomin Da Budurwa Take Nunawa Idan Tana Son Namiji 

Kallon ido: Idan mace tana yawan kallon idonka ba tare da kiftawa ba, akwai yiwuwar cewa ta na sonka. Idan ta Kalle ka tana murmushi cikin jin Kunya, yana nuna ta kamu da shaukin ka.


Kai da komo a inda kake zaune, yana daga cikin nuna alamomin idan mace na son namiji za ta dinga kai komo a duk inda ta san kana zama. Kuma za ta dinga yin kyakykywar shiga da yin kwalliya don ta nuna maka alamar tana kaunarka. 


Idan budurwa tana son namji tana kokarin yin wasu abubuwa da zai sa su dinga yin magana da juna. Ko kuma ta yi kokarin hada alaka da wanda ke da kusanci da namijin da take so. 


Wannan wasu ne daga cikin alamomin da budurwa ke yi idan ta kamu da soyayyar namiji, amma baza ta iya bayyana masa ba sai ta wadannan hanyoyin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post