Hukuncin wasa da azzakari har a fitar da maniyyi

Hukuncin wasa da azzakari har a fitar da maniyyi
Hukuncin wasa da azzakari har a fitar da maniyyi 


Likitoci masu ilimin Sanin Lafıyar jikin Bil-Adama sun fadi hukuncin wasa da azzakari da yin wasa da gaba yake haifarwa


Dab'iar yin wasa da azzakari da yin wasa da gaba don a fitar da maniyyi ba abune mai kyau ba. Amma yanzu wannan dabia ta zama ruwan dare ga samari da yan mata. Kuma babbar matsala ne sosai ga lafiya, sannan kuma hukunci ne maigirma a musulunce ga masu aikata hakan. 


Yin wasa da azzakari har a fitar da maniyyi bai halatta ba, Kuma yana daga cikin manyan laifuka a Musulunci kamar yadda Malamai suke yawan yin bayani akan hakan. Don hukuncin yin wasa da azzakari da Samari Ke yi da kuma yin wasa da farji da mata ke yi, yana jawowa mai yin hakan fushi da kuma tsinunwa daga ubangiji (SWT).


Manzon Allah SAW yana cewa: "mutane 7, Allah ya tsine musu. Kuma ba zai dube su da rahama ba a ranar alkiyama ba. Sannan zai ce musu: "ku shiga wuta tare da masu shigarta". Jerin mutanen da Allah ya tsine musu;


1. Mai aikata Luwadi. Wato wanda yake amfani da dan uwansa namji ta dubura don ya biyawa kansa bukata har ya fitar da maniyyi. Allah ya tsare mu 


2. Mutumin da ake aikata Luwadi dashi, wato wanda yake bada duburar sa a saka azzakari a ciki har a biya bukata. 


3. Mutumin da yake yin Zina da dabbobi, akwai mutanen da suke amfani da dabba su saka azzakarinsu a duburar dabba har su fitar da maniyyi. 


4. Mutumin dake aikata zina da uwa sannan kuma ya yi da yarta, suma wannan Allah ya tsine musu. 


7. Wanda yake yin Zina da hannayensa (mai yin wasa da azzakarinsa har ya fitar da maniyyi da kuma Mace Mai yin Hakan ga al'aurarta). Wanda irin hakan ake kira da istimna'i. 


Sannan Kuma Shi irin wannan Aikin yana daga cikin irin Laifukan da Mutanen Annabi Lut (as) Suke yi. Shiyasa Allah S.W.T ya hukunta su saboda dabiar da suke aikatawa ta Luwadi. Wato tun daga nan za mu gane hukuncin masu aikata wannan dabia. 


An Ruwaito cewa duk masu yin haka idan basu tuba ba, za su tashi a ranar alqiyama hannayansu sun dauki ciki (juna biyu).


Likitoci masu ilimin Sanin Lafıyar jikin Bil-Adama sun fadi hukuncin wasa da azzakari da yin wasa da gaba yake haifarwa:


1. Raunin Ido: masu yin wasa da gaba don fitar da maniyyi suna iya samun barazanar raunin ido idan basu dena ba, sukan makance kafin wani lokaci mai nisa.


2. Mantuwa. Yin wasa da azzakari da yin wasa da farji ga mace yana haifar da saurin mantuwa (mantuwar karatu, etc).


3. Rashin Haihuwa: yana daga cikin hukuncin wasa da azzakari haifar da daskararren Maniyyi, yana kashe kwayoyin halitta daga jikin Namiji ko mace masu wasa da gaban su don fitar da maniyyi. 


4. Raunin Al'aura: Duk masu yin haka, idan suka yi aure, sukan yi fama da rashin karfın Azzakari, saboda duk Maniyyin da aka fitar dashi da-gan-gan, Ba ya fita gaba-daya. Wannan wanda ya saura, Sai ya daskare  a cikin Marar mutum. 


5. Ciwon Hauka: da kuma Kaskanci. Masu aikata yin wasa da al’aurar su na iya fuskantar ciwon hauka idan basu daina ba. 


Wannan kadan ne daga cikin hukuncin wasa da azzakari da yin wasa da al’aura, illolin suna da yawa sosai wanda masu aikata wasa da gabansu mace ko namiji kan iya fuskanta. Da fatan Allah ya shiryi duk masu aikata wannan dabia ta yin wasa da azzakari da wasa da farji.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post