Hukuncin wanda yayi mafarki yana azumi |
Babu wani dalili da yazo cewar fitar da maniyyi kadai yana karya azumi ba tare da jima'l ba.
Mallam don Allah menene hukuncin wanda yayi mafarki har ya fitar da maniyyi a lokacin da yake yin azumi? Sannan Menene hukuncin wacce take magana da mijinta ko kuma suka kalli juna bada niyyar sha'awa ba amma kuma sai sha'awar ta motsa har takai da fitar ruwa maniyyi?
Hukuncin wanda yayi mafarki yana azumi
Wanda yayi mafarki a watan azumi mace ko namiji azumin sa yana nan koda kuwa yafitar da maniyyi, domin an dauke alkalami akan mutumin da yake bacci har sai bayan ya FARKA daga bacci da yake yi.
Ita kuma hukuncin matar da ta kebe da mijinta har sha'awar su ta motsa amma kuma sai sha'awar ta motsa har takai da fitar ruwa maniyyi, za taci gaba da azuminta babu komai. Domin Jabir bin Zaid (R.A) yace:
"Wanda ya kalli mace ya fitar da maniyyi yaci gaba da azuminsa babu komi a kansa.
Wannan shine abinda Imam Shafi'l (Babban almajirin Imam Malik), da Imam Thauri da Auza'iy duk suka tafi akai sunce:
Babu wani dalili da yazo cewar fitar da maniyyi kadai yana karya azumi ba tare da jima'l ba.
Amma jima'l ko an fitar da maniyyi ko ba'a fitar ba yana karya azumi, kuma akwai kaffara akai.
Duba sharhin Bukhari ibn Buddal, Juz'ina hudu, shafi na 59).
Hakanan wanda ya kalli matarsa har yafitar da maziyyi shima azuminsa yana nan.
Amma mazhabar malikiyya suna ganin fitar maniyyi ta hanyar kallo ko runguma yana karya azumi, kuma akwai ramuwa da kaffara akai. Amma maziyyi akwai ramuwa kawai babu kaffara. Domin suna kafa hujja da cewa abinda ake bukata a jima'i shine fitar da maniyyi, saboda haka fitar maniyyi din, daidai yake da jima'l.
Saidai sauran manyan malamai sunyi masu raddi cewa:
"Hukuncin da nassi yazo dashi ya ambaci jima'ine kawai ba fitar da maniyyi ba, kuma suka cigaba da kafa hujjar cewa idan da mutum zaiyi jima'l ba tare da ya fitar da maniyyi ba ai zai rama azumine kuma yayi kaffara, kuma da fitar da maniyyi ne, da sai ace mai barci ma idan yayi mafarki yafitar da maniyyi shima yayi kaffara kenan."
Munji hukuncin wanda yayi mafarki yana azumi, da kuma hukuncin fitar da maniyyi ba tare da an yi Jima'i ba. Sannan kuma munji bayani kan hukuncin yin jima’i ba tare da fitar da maniyi ba a lokacin azumi.