Herbert Wigwe Shugaban Banki Access Bank |
Herbert Onyewumbu Wigwe CFR wanda ya mutu a ranar 9 ga watan Fabrairu 2024 ma'aikacin banki ne kuma ɗan kasuwa ɗan Najeriya.
Kafin Allah yayi masa cikawa ya dauki dawainiyar marayu dubu 30 ya mayar da su kamar ya'yansa.
Ana kallon Wigwe, wanda ya mutu yana da shekara 57, a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka kawo gagarumin sauyi a tsarin bankunan Nijeriya, inda ya taɓa yin aiki a Guaranty Trust Bank a matsayin darakta kafin ya tafi Access Bank.
Herbert Onyewumbu Wigwe CFR wanda ya mutu a ranar 9 ga watan Fabrairu 2024 ma'aikacin banki ne kuma ɗan kasuwa ɗan Najeriya. Ya kasance babban daraktan hukuma kuma shugaban bankin Access Plc, daya daga cikin manyan cibiyoyin banki guda biyar a Najeriya, bayan ya gaji abokin kasuwancinsa, Aigboje Aig-Imoukhuede.
A watan Oktoban 2022, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba shi lambar yabo karramawar CFR na Tarayyar Najeriya.
Bayan kasuwanci da tsarin sa, Wigwe ya kasance mai taimakon jama'a. A cikin 2016, ya ƙaddamar da gidauniyar HOW. Gidauniyar Wigwe tana taimakawa da ƙarfafa matasa da kuma daukar dawainiyar marayu samada dubu 30, da kawar da cutar zazzabin cizon sauro, cutar kansar prostate, fa yara.
Ya mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar 9 ga Fabrairu 2024 a Amurka a kan hanyarsa ta halartar gasar Super Bowl LVIII na Lahadi a Las Vegas.
Ya rasu ya bar ‘yan’uwa hudu, da mahaifinsa, wanda zai cika shekara 90 a bana, sai kuma mahaifiyarsa.