Falalar Goman Karshe Na Watan Ramadan Ga Al'ummar Musulmin Duniya |
Falalar daren lailatul kadri dare ne mai girma wanda a cikinsa ne Allah Ta'ala ya saukar da Al-Qur’ani. Annabi Muhammadu ( ﷺ ) ya yi bayanin cewa ana samun daren a cikin goman ƙarshen Ramadan
Ga shi dai kwanakin Ramadan suna ta gudu, muna daf da shiga goman karshe wanda shi ne dama ta karshe ga wanda ya yi sakaci a farkon watan, ko kuma ya zama cika alheri ga wanda ya kyautata ya bayar da abin da ake so a baya.
Goman karshe na watan Ramadan kasuwa ce babba da masu tsere suke tsere a cikinta. Lokaci ne da wanda ya yi sakaci ke matsuwa a cikinsa, ake jarraba masu himma a cikinsa, ake tantance ma’abuta Lahira da ma’abuta duniya.
Hadisi ya tabbata daga Uwar Muminai Aisha (RA) cewa “Manzon Allah (SAW) ya kasance idan goman ƙarshe na watan Ramadan ta shiga, Ya kan raya dararanta gaba ɗaya ma'ana ba ya barci, Sai ya tayar da iyalan sa su tashi su yi ibada, Kuma ya ɗaura mayafin sa ma'ana ƙara ƙoƙari. Har ila yau, A cikin dararan ne ake samun babbar garaɓasar nan ta daren Lailatul Qadri.
Falalar daren lailatul kadri dare ne mai girma wanda a cikinsa ne Allah Ta'ala ya saukar da Al-Qur’ani. Annabi Muhammadu ( ﷺ ) ya yi bayanin cewa ana samun daren a cikin goman ƙarshen Ramadan cikin mara (kwanukan da za a kirga a samu ragowar daya a ciki wato 21, 23, 25, 27, 29). Abdullah bin Abbas (RA) Ya ce Allah Ta'ala ya saukar da Al-Qur’ani gaba ɗaya daga lauhil mahfuz zuwa sama ta ɗaya a cikin daren lailatul kadri. Daga nan ne Mala’ika Jibrilu ya riƙa sauko da shi Aya-Aya ko Sura-Sura kamar dai yadda Allah ya umurce shi ya yi.
A wani ƙaulin ana cewa Mala’ika Israfilu ne ya ɗauko Al-Qur’ani daga Allah zuwa Lauhil Mahfuz, su kuma Mala’ikun da ake kira da Kiramun Barara suka ɗauko shi zuwa sama ta ɗaya, daga nan shi kuma Mala’ika Jibrilu ya riƙa sauko da Wahayinsa ga Annabi Muhammadu ( ﷺ ), Allah Ta’ala ya albarkaci mu al’ummar Annabi Muhammadu ( ﷺ ) fiye da sauran al’ummomin da suka gabata kamar yadda rayuwar mai gidan namu Annabi Muhammadu ( ﷺ ) ta fifici ta sauran Annabawa.
Allah Madaukakin sarki yana cewa “LALLAI MU MUKA SAUKAR DA WANNAN ALQUR’ANIN A DAREN KADDARAWA, WAYA SANAR DA KAI GAME DA DAREN KADDARAWA?
SHINE DARE DA YAFI WATA DUBU”
A kan haka ne Allah ya ba mu Daren Lailatul Kadri wanda ya fi watanni 1000, kimanin sama da shekara 83. A ko wace shekara, Duk Musulmi idan ya yi Ramadan tare da ƙudurcewa a ransa na samun daren (walau ya gani ko bai gani ba), Allah zai rubuta masa ladan daren. Wannan yana nuna cewa a duk Ramadan, Muna da shekara 83 da ƴan kai kari a kan shekarun mu. Misali, idan mutum ya riski Ramadan sau 40, Yana da ƙarin shekaru na ibada dare da rana masu albarka zalla 83 sau 40 wanda zai bashi jimillar shekara dubu uku da ɗari uku da ashirin (3320). Wannan falala ce ta Allah ga mu al’ummar Annabi Muhammadu ( ﷺ ).
Sufyanu Suri (Rahimahullah) ya ce, “An so idan goma karshe ya shigo (Musulmi) ya yi kokari da daddare ya yi kokari a cikinsa, ya tashi iyalinsa da ’ya’yansa su yi Sallah matukar za su iya hakan.”
Abu (RA) Hurairah ya ruwaito daga Manzo (SAW) cewa “DUK WANDA YA RAYA DAREN LAILATUL QADRI DA IBADU DA ZIKIRAI BABBA KO KARAMI ALLAH ZAI GAFARTA MASHI ZUNUBAN SHI BAKI DAYA”
Ku gabatar da aikin alheri ga kanku, ku tsayu kuma ku yi kankan da kai. Uwar Muminai A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce: “Ya Manzon Allah! Shin idan na riski daren Lailatu Kadri me zan ce a cikinsa? Sai ya ce: “Ki ce: “Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa, fa’afu anni.” Ma’ana “Ya Ubangiji! Kai Mai yawan afuwa ne, Kana son afuwa, Ka yi min afuwa.” Ku yawaita wannan addu’a a cikin goman karshe. Ubangijinmu Ya ce, “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai ne Ni ina kusa, Ina amsa kiran wanda ya yi kira idan ya kira Ni. Don haka su amsa Min, kuma su yi imani da Ni, damaninsu suna shiryuwa.”
Ko kun san su wane ne wadannan bayi? Halittu dukkansu bayin Allah ne, sai dai kuma wadannan bayi kebantattu ne. Su ne bayi daga ma’abuta addu’a, bayin da suke jiran a amsa musu, su ne masu addu’a cikin kankan da kai, masu addu’a tare da babbar fata, masu kankan da kai wajen kwadayin amsawa; “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to, lallai Ni ina kusa.