Amfani Ganyen Yadiya Ga Lafiyar Dan Adam |
Yadiya da Kuli-kuli abinci ne ga mutanen arewacin Najeriya Yadiya ganye ne mai amfani a jikin dan adam.
Ganyen Yadiya ganyene launin kore wanda yake tsirowa aana samun sa a mafiyawan jihohin arewacin Najeriya. Yadiya tana tsirowa ta yadu akan doron kasa bata damu da ruwan sama ba, takan tsiro ne ko ba ruwan sama a lokacin rani.
Ana shanya ganyenta idan ya bushe a dake a maida shi gari, sai a rinka sanya cokali daya karami a cikin kunu mai dumi a sha.
Domin maganin
Hawan jini
Ciwon daji na fata
Iskan dake kumbura jiki.
Kumburi da cwon ciki
Maganin guba (Poison)
Maganin dafin maciji.
Maganin sanyin mata na syphillis.
Maganin ciwon mara da zafin fitsari ga maza da mata.
Maganin raunin mazakuta ga namiji.
Kurajen cikin baki dana harshe
Karamcin sinadirran Vitamins.
Karin jini da karfin jiki
Maganin basir mai tsiro.
Ana amfani da ruwan bayan an dafa domin warkarda gembo a jiki. Ana wanka da ruwan ganyen Yadiya domin maganin karzuwa da kurajen fatar jiki.