Abubuwa 5 da Mace ke yi idan ta kamu da son ka |
Idan mace na son ka bata iya boyewa, akwai wasu abubuwa 5 da suke yi wanda Zakai saurin fahimtar irin son da take yi maka
Idan wani ya damu da kai, zai nuna hakan ta hanyar ayyukansa. Wannan gaskiya ne musamman idan duka abokan tarayya suna jin iri ɗaya game da juna.
Ga abubuwa 5 da mace ke yi idan ta Kamu da son ka:
1) Za Ta Bada Lokacin ta akan ka: Idan ta fara ɓata lokaci mai yawa tare da kai, alama ce ta kulawa da nuna kauna. Domin idan bata damu da kai ba bazata so ta yi minti 2 tare dakai ba.
2) Tana So A Ganta Tare Da Kai: Idan tana son a ganku tare a bainar jama’a, yana nufin tana alfahari da kasancewa tare da kai. Kuma tana alfahari kan duk wanda zai ganta tare da kai.
3) Za Ta Kawo Maka Abinci: Girka maka abinci hanya ce mai dadi da za ta iya nuna maka tana son ka. Idan mace na yi maka girki tana baka ba tare da ka nemi hakan ba wannan yana nuna tsantsar kauna.
4) Za Ta Faɗa Wa Kawayenta Game Da Kai: Idan mace tana yawan yin zancen ka a cikin kawayenta tana bayyana musu muhimman abubuwa game da kai, alama ce ta gaske tana son ka.
5) Za Ta Gabatar Da Kai Ga Kawayenta Na Kusa: Idan mace tana son ka za ta yi kokarin sadaka da manyan kawayenta, Saduwa da kawayenta na kusa mataki ne mai girma kuma yana nuna ta amince da kai.
Ka tuna, waɗannan ayyukan na nufin tana buɗe zuciyarta a gare ka, tana nuna ta amince dakai a zuciyarta, tana nuna maka ta shirya auren ka. Wannan shine ake kira so na hakika da mace ke yi maka.