Abubuwa 3 Da Idan Mace Na Yiwa Namiji Daya Daga Ciki Zai Daina Sonta

Abubuwa 3 Da Idan Mace Na Yiwa Namiji Daya Daga Ciki Zai Daina Sonta
Abubuwa 3 Da Idan Mace Na Yiwa Namiji Daya Daga Ciki Zai Daina Sonta 


Akwai abubuwan da mace ke yi da ke jawo miji ko saurayi ya daina nuna mata kauna 

Namiji zai daina sonki idan kika masa abubuwa uku: Shin kinsan abubuwan da idan kika yiwa mijinki ko saurayinki duk irin kaunar da yake yi miki zai daina? 


Wasu matan na tunanin cewa shi so ya wuce komai, idan namiji yana son su suna tunanin duk abinda za su yi masa ba zai jawo ya daina son su ba. Hakane akwai abubuwan da idan mace ta yiwa namiji yana iya kau da kansa idan yana kaunarta. Sai dai akwai wasu abubuwa 3 wanda duk irin yadda namiji yakai ga son mace idan tana yi masa su zai daina kaunar ta. 


Abubuwa 3 Da Idan Mace Na Yiwa Namiji Daya Daga Ciki Zai Daina Sonta 

1- Rashin gode masa a duk lokacin da ya tallafa miki. Shi namiji yana son idan yaiwa mace abu ta yaba masa ta Kuma gode masa, rashin yin hakan nasa ki fita a ransa duk kuwa da irin kaunar da yake yi miki. 


2- Tilasta mishi yin abinda yafi karfi samun shi. Akwai matar da idan ta fuskanci miji na kaunar ta tana iya tilasta shi yai mata abinda bashi da ikon yi. Wannan dalilin nasa namiji ya daina son ki. 


3- Laifi mafi girma shine ki zage shi. Wannan kuma karshen raini Kenan, duk irin son da namiji ke yi miki idan har za ki zage shi to son ki da kaunar da yake yi miki za ta fita daga ransa. 


Dayawa daga cikin magabata sunce duk Namijin da ya rabu da mace saboda zagin shi da tayi, to bazai kara sonta kamar yadda ya sota a baya ba, koda su ma'aurata ne.


Wadannan sune abubuwa 3 da idan mace na yiwa namiji zai daina son ta gabaki daya, duk irin kaunar da miji ko saurayi ke yiwa mace idan har tana yi masa daya daga cikin wadannan abubuwan da muka bayyana zai daina kaunar ta. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post