Abinci 5 Da Cin Su Ke Karawa Namiji Karfi Dan Sha'awar Son Jima'i |
Nau'in Abinci 5 Dake Kara lafiya, Kuzari da sha'awar son Jima'i ga maza
Akwai nau'in abincin da ake so maza su dinga yin ta'ammali dasu idan suna son samun kara karfi da sha'awar son jima’i. Nau'in abincin suna da yawa amma za mu kawo muku wadanda suka fi mahimmanci kuma suke da saukin siya.
Abinci 5 Da Cin Su Ke Karawa Namiji Karfi Dan Sha'awar Son Jima'i
1. Ayaba(Banana); ayaba na daga cikin nau'in abincin dake kara girman gaban namiji, idan kana son girman gaba da tsayi, ka dinga cin Ayaba akai-akai. Sannan kuma tana kara karfi da Kuzari ga namiji.
2. Nama (Meat); Idan Kana son Kara karfin jima’i, ka dinga cin nau'in nama musamman naman sa, naman kaji, don suna dauke da sinadarin The amino acids L-arginine da suke taimakawa wajen saurin gudanar jini a jikin dan adam. Mace da namiji na bukatar saurin gudanar jini don aiwatar da jima’i.
3. Fiya (Avocado's) fiya wanda a turance ake kira da avocado yana samar da Kuzarin da ake bukata na aiwatar da komai, har jima’i. Wannan dan itacen na dauke da sinadarin folic acid dake taimakawa saurin gudanar jini a jikin dan adam.
4. Jan Inabi (Red Grape) cin Inabi na taimakawa maza bukatar son yin Jima'i. Idan Kana cin ya'yan Inabi za kaji kana sha'awar son Jima'i. Yana taimakawa wajen motsa sha'awa.
Cin Inabi da safe zai taimakawa maza su ji bukatar son saduwa da mace a lokacin kwanciya bacci. Don haka ne masana lafiya suka shawarci maza da fama da karancin sha'awa da su dinga shan Inabi.
5. Abinci Mai gina jiki, cin abinci mai gina jiki na daga cikin nau'in abincin dake kara sha'awa da son yin Jima'i. Ka dinga cin abinci wanda aka sarrafa da miya mai kyau da kayan hadi irin na ganye dake kara lafiya da Kuzari.