Yadda Hisbah ta cafke fitacciyar Yar madigo Princess Ramlat

Yadda Hisbah ta cafke fitacciyar Yar madigo Princess Ramlat
Princess Ramlat 


Hukumar Hisbah a Kano ta cafke fitacciyar Yar madigo Princess Ramlat 

Hukumar Hisbah takama Ramlat princess, fitacciyar ƴar maɗigo, wacce ta yi bidiyon da take tallata kanta take cewa duk namijin da zai aure ta sai ya auro mata macen da za su dinga lalata da ita.


A kwanakin baya da suka gabata wani faifan video yai ta yawo a shafukan social media inda princess Ramlat ta fito tana bayyana cewa duk namijin da zai aure ta sai ya auro mata macen da za su rinka lalata da ita.


Wannan yasa hankalin al'umma da dama ya tashi inda akai ta kira ga mahukunta da su dauki matakan da suka dace don kawar da masu irin wannan badala. 


Sai dai a ranar Alhamis Hukumar Hisbah ta Kano ta sanar da kama Ramlat Princess, wanda jama'a ke ta nuna jindadin su kan kamun da akai mata tare da fatan hukunta ta don ya zama darasi ga masu aikata hakan anan gaba. 


Me Za Ku Ce?


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post