Yadda Ake Yin Hadin Sassaken Baure Na Matan Aure |
Hadin Sassaken Baure (TSALLE DAYA)
Wannan hadin yana taimakawa (Motsa sha'awa da kara ni'ima da kashe kwayoyin cuta) ga matan aure musamman wanda ke son Kara Samun karbuwa daga wajen mazajensu.
Wannan hadin hadine na musamman wanda mace tana amfani dashi zata kara samun wadatacciyar ni'ima, sannan duk yana kashe kwayoyin cutar gaban mace.
Yadda Ake Yin Hadin Sassaken Baure Na Matan Aure
Don yin wannan hadin ana samun wadannan abubuwa kamar haka;
- Sassaken baure
- Mazarkwaila
- Zuma
- Kanunfari
- Citta
Zaki zuba sassaken baure a cikin tukunya, ki zuba ruwa da yawa. Sai ruwan ya kusa shanyewa sai ki sauke ki cire sassaken bauren. Ki zuba zuma da mazarkwaila da kanunfari da citta. Ana son a zuba kanunfari dai dai misali, ki mayar acikin tukunya ya kara tafasa, sannan ki juye ki rinka sha kofi biyu a rana safe da yamma. Za kuma ki iya daka yaji da wannan sassaken bauren.