Yadda Ake Yin Hadin Dabino (Idona Idonka) |
Hadin Dabino (MAI SONA IDONA IDONKI)
Wannan wani hadine wanda ke sa miji kyautar da beyi niyyaba. Ki yi kokarin yiwa mijinki wannan hadin done ke kanki za ki sha mamaki sosai. Ki samu wadannan abubuwa kamar haka;
- Dabino
- Zuma
- Tatacciyar madara
- kanunfari
Ki nuka kanunfari ko ki daka shi ya daku sosai. Sannan ki zuba busasshen dabino ya daku sosai, ki samu tatacciyar madara ki zuba cokali uku na wannan garin dabino da kanunfari kisha kayanki.
Hadin Dabino Kashi Na Biyu (MAI SUNA MIJIN HAJIYA)
Wannan hadin mace da mijinta duk suna iya amfani dashi domin karin ni'ima da sha'awar juna.
Za'a jika dabino a cire kwallayen, ki saka a cikin fridge ya samu kamar kwana uku sai ki dame shi ya zama kamar fura ki hada da ruwan kwakwa da zuma ki rinka sha.
Hadin Biskit (MAI SUNA TAMBARI)
(Karin ruwa da sha'awa)
Wannan hadin mace da namiji duk suna iya amafani dashi domin karin ruwan gaba da sha'awa batare da gajiyawa ba. Zaki samu wadannan kayan hadin;
- biscuit
- madara ko nono
- farin garin rogo na yin dan wake
- aya manya
- gyada
- alewar mata
- garin dabino
Zaki soya ayarki sama-sama, sai ki gyara gyada ki cire bawon. sannan ki hade su guri guda tareda sauran kayan hadin ki dake su, ko ki nika. sai ki rinka diba kina sha a madara ko a nono. Ana son komai ya kasance yazama daidai.
Hadin Zogale (MAKALE MATA)
(Zaburar da mace wajen sha'awa da karin juriya batare da gajiyawa ba).
- Danyen zogale (ganyensa)
- Madara peak
- Zuma
- Kanunfari
Zaki gyara ganyen zogale ki wanke ki dafa ki markade shi, sai ki tace ki zuba garin kanunfari ki zuba madara ta ruwa da zuma ki rinka sha da safe da yamma. Zaki sha mamaki.