Yadda Ake Yin Gyaran Kafa Don Amarya |
Ina amaren dake shirin yin aure? Ga Yadda Ake Yin Gyaran Kafa
A topic din mu na baya na yi muku bayani kan hanyoyin Yadda ake yin gyaran jiki, gyaran fata da gyaran gashi. Yau kuma na zo muku da hanyoyin Yadda ake yin gyaran kafa musamman ga amarya dake shirin yin aure, har matan dake gidan aure ma suna iya yi.
Gyaran Kafa Na Daya (SHI AKE KIRA SUMUL)
Bake ba zuwa wajen wanke kafa muddin kinyi amfani da wannan hadin, domin kuwa yana karawa mace kyau ya gyara mata kafa. Ki samu wannan abubuwan kamar haka;
- Man shanu
- Man kwakwa
- Man ridi
- Man alayyadi
Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi, da daddare zaki hada wadannan mayukan guri guda ki shafa a Kafar lokacin da zaki kwanta bacci, ki daure kafar da leda ki sa safa. Da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi.
Gyaran Kafa Na Biyu 2 (MAI SIMINTI)
Shima wannan hadin na musamman ne, ana yinsa da wannan abubuwan;
- Man kwakwa
- Man shanu
- Man zaitun
Ki hada man kwakwa da man zaitun guri guda. Sai ki shafa da daddare, da safe ki dan gasa kafar sannan ki wanke ki shafa man zaitun.
Gyaran Kafa Na Uku 3 (MAI AUDUGA)
Shima wannan hadin yana da kyau sosai domin yana gyara kafa ta yi fes. Ku samu
- kokumba
- Lalle
- Man ridi
Ki hada ruwan kokumba da lalle guri guda, ki shafa a kafa da safe ki wanke, ki shafa man ridi. Yana taimakawa wajen gyara kafa ta yi kyau tai fes.
Wadannan sune hanyoyin yadda ake gyara kafa ta yi kyau, ina fatan kun amfana daga wadannan hanyoyin domin za su taimaka muku wajen gyara jiki musamman ga yan matan dake shirin zama amarya.