Yadda Ake Yin Gyaran Gashi Na Musamman Don Mata

Yadda Ake Yin Gyaran Gashi Na Musamman Don Mata

Yadda Ake Yin Gyaran Gashi Na Musamman Don Mata 


Hanyoyin Yadda Ake Yin Gyaran Gashi Na Musamman Don Mata 


A darusan da suka gabata na baya na kawo muku hanyoyin yadda ake yin gyaran jiki da gyaran Fata wanda mata za su yi amfani dashi don inganta jikinsu musamman a wajen mazajensu. 


Gyaran Gashi Na Daya 1

Wannan hadin shi ake cewa 'anty yalash'. Domin kuwa gashinki bashi ba karairayewa, kuma zai rinka laushi kuma ya kara tsawo.


Ana daka ganyen magarya a rinka wanke gashi dashi. Yana kara karfafa gashi ya kuma hanashi zubewa. Sannan sai a rinka shafa man kwakwa.


Gyaran Gashi Na Biyu 

Shima wannan hadin yana gyara gashi ya saka shi yin kyau sosai, ku samu wannan abubuwan;

  • Man zogale
  • Man kwakwa
  • Man zaitun

Zaki hadesu guri guda ki rinka shafawa a kanki. Yana kara tsawo da laushi gashi. 


Gyaran Gashi Na Uku 3

Ki yi kokarin yin wannan idan har kina son gyara gashi ba tare da ya karye ba. Ana samun wannan abubuwan;

  • Man zogale
  • Ganyen magarya
  • Man kanunfari kadan

Sai ki hadesu guri guda ki rinka shafawa a kanki. Yana sanya tsayin gashi ya kuma sashi laushi. العالم


Gyaran Gashi Na Hudu (SIRRIN KENAN)

Shima wannan hadin gyaran gashin yana da kyau sosai, 

  • Ruwan tumatir
  • Sabulun salo

Zaki matse ruwan tumatur sai ki zuba sabulun salo aciki ki barshi ya yi kamar minti 10, Idan ya jika sai ki shafa a kanki da daddare, idan zaki kwanta bacci. Da safe sai ki sanya ruwan dumi ki wanke sannan ki shafa man kwakwa.


Gyaran Gashi Na Biyar (NA ZARCE SA'A)

Wannan hadin shi ake cewa 'na zarce sa'a, domin kuwa gashinki bashi ba karairayewa, kuma zai rinka laushi kuma ya kara tsawo.

  • Man gyada
  • Man alaiyadi
  • Man zaitun
  • Man kwakwa
  • Lalle
  • Man albasa
  • Man hulba
  • Man ridi

Zaki hada man hulba da lalle guri guda ki tafasa, sai ki tace ki wanke kai dashi, sannan ki nemi sauran mayukan ki rinka shafawa akai. Zaki sha mamaki insha Allah.


Gyaran Gashi Na Shida 6 (DA HAKA NA GAGARA)

Shi wannan ana yi masa lakabi da "Haka na gagara" saboda yana da kyau sosai, ku samu wannan abubuwan;

  • Danyen kwai
  • Sabulun salo
  • Garin shammar

A fasa kwai, amma banda kwanduwar, farin kadai zakiyi amfani dashi, sai ki zuba sabulun salo aciki, ki matse shi ki zuba garin shammar aciki. Sai ki wanke kai. Sannan ki samu man gyada mai kyau da na kwakwa ki shafa.


Wannan sune hanyoyin yadda ake yin gyaran gashi wanda mata za su dinga yi, a tabbatar idan kuna amfani da wasu daga cikin wadannan hanyoyin za ku samu biyan bukata.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post