Yadda Ake Yin Addu'ar Istikara

Yadda Ake Yin Addu'ar Istikara
 Yadda Ake Yin Addu'ar Istikara 


Muhimmiyar Addu'a Ta Istikara 


Imam Bukhari ya ruwaito acikin littafinsa na sahihul bukhari, mutumin dake neman zabin Allah akan wani al-amari wanda ya shige masa duhu, kasuwanci yakeso ya fara yana neman zabin Allah, samari ne sukayi miki yawa kina neman zabin Allah acikinsu wanda zaifi zama alkairi da auransa. Ko kuma aure zakayi cikin 'yan mata da yawa kana neman zabin Allah wacce tafi zama alkairi a gareka, ko kuma tafiya zakayi ko aiki kake nema aka baka zabi. Koma dai menene kake/kike nema a rayuwarki.


Kanaso Ubangiji ya zaba maka abinda yafi alkairi a gareka, ba sai kaje wajen wani malami ba yayi maka duba ko ya bincika maka, kai da kanka zaka iyayin addu'a domin Allah ya zaba maka abinda yafi zama alkairi agareka.


Jabir Ibn Abdullah RA yace Annabi (SAW) yana koyar damu istikara kamar yadda yake koyar damu surah acikin al qurani mai girma, ya nanata mana har sai mun iya. Kakan tashi cikin dare kayi alwala sannan kayi nafila raka'ah biyu. Malamai sukace zakayi niyya da niyyar istikara. Wasu malamai sukace akanso acikin nafilar ka karanta suratu yasin, raka'ar farko ka karanta rabi ta biyu ka karasa da rabin. Bayan kayi sallama malamai sukace an zabi ka karanta suratul kafirun da ikhlas da ayatul kursiyyu da karshen suratul baqara; amanar rasulu, sannan sai ka karanta suratul Qasas (ayata 68-69), sai kuma suratul Ahzab (ayata 36). Sannan sai ka karanta wannan addu'ar kamar haka;


اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرِكَ بِعِلْمِكَ وَأَسْتَقْدِرُكَ بَقُدْرَتِكَ وَ أَسْأَلُكَ مِن فَضْلِكَ العظيم, فَإِنَّكَ تَقَدْرُ وَلا أَقْدَرُ, وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَمُ وَ أَنْتَ عَلَامُ الْغُيُوبِ اللَّهُمَّ إِنْ كُنتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ يَجُوزُ أَنْ يُسْمَى حَاجَتَهُ أَوْ يَكْتَفِي بِنِيَهِ وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِهَا خَيْرًا لِّي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي وَ عَاجِلِ أَمْرِي وَ آجِلِهِ), فَقَدَّرْهُ لِي وَيَسْرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ, وَ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرُّ لَي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي وَ عَاجِلِ أَمْرِي وَآجِلِهِ, فَاصْرِفْهُ عَنِّي

وَاصْرِفْنِي عَنْهُ، وَاقْدِرْ لِي الْخَيْرَ خَيْثَ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بَهِ"


"Allahumma inni astakhiruka bi ilmika wa astaqdiruka bi qudratika, wa as'aluka min fadlikal azim, fa innaka taqdiru wala aqdiru, wa ta'alamu wala a'alam wa anta allamul guyub. Allahumma in kunta ta'alamu anna hazal amru (yakamta ya fada bukatansa anan ko ya bayyana shi, Allah shine masani), khairan li fi dini wa ma'ashi wa aqibatu amri (wa ajili amri wa ajilihi), faqdirhu li wa yassirhu li, thumma barik li fihi. Wa in kunta ta'alamu anna hazal amru sharrun li fi dini wa ma'ashi wa aqibatu amri (wa ajili anıri wa ajilihi), fasrifhu anni wasrif ni anhu, waqdur liyal khairu haithu kana thumma ardini bihi"


Anaso ayi addu'ar nan cikin dare ko kuma in za a kwanta bacci. Anaso arinka yinta akai-akai ba lallai sai kayi mafarkin ga ganin abin ya faru ba. Allah zai iya nunamaka ko kuma kaji zuciyarka ta nutsu da sannan Allah ya tabbatar dashi zakaga abin yazama alkairi gareka da jama'arka.


Addu'ar Saeed Ibn Jubair 

Addu'ace da malamai suke mata kirari da suna' dare daya Allah kanyi makaho'.


Saeed Ibn Jubair yace bai taba ganin wata addu'a ba wacce duk abinda yakeson Allah SWT ya bashi da zarar ya roki Allah da ita yake samu nan take.


Malamai sukace akanso kayi alwala kayi nafila duk yadda tasamu sannan ka fuskanci alqibla ka karanta suratul Fatiha adadi mai yawa, Ayatul kursiyyu itama haka, suratul Qadr itama haka, suratul Ikhlas ma haka. Ka iyayin kafa 100 ko kuma 300, duk dai yadda ya samu sannan sai ka karanta wannan addu'ar kamar haka;


قُلِ اللَّهُمَّ فَاطِرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ عَالِمَ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ أَنْتَ تَحْكُمُ بَيْنَ عِبَادِكَ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ"


"Qulillahumma fadiras samawati wal ardi alimul gaibi wash shahadati, anta tahkumu baina ibadika fima kanu fihi yaktalifun"


(Abu Musa Al-madin ya ruwaito acikin littafinsa JALA'ILIL AFHAM).


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post