Yadda Ake Warkar Da Mara Lafiya Ta Hanyar Addu'a

Yadda Ake Warkar Da Mara Lafiya Ta Hanyar Addu'a
 Yadda Ake Warkar Da Mara Lafiya Ta Hanyar Addu'a 


Yake 'yar uwa idan ki kayi wannan addu'ar kamar yadda Manzon Allah SAW yayi akan kowane irin ciwo ne, Allah zai yaye masa ciwon cikin dan kankanin lokaci Insha Allahu mu jarraba abun mu gani.


Hanyoyin da Manzon Allah SAW ke warkar da marasa lafiya ta hanyar addu'a.


Akwai hadisin Bukhari da Muslim da aka ruwaito daga Aisha RA tace. "Idan mutum yazo gurin Manzon Allah SAW, ya kawo masa kukan yaji rauni ko wani guri yana masa ciwo a jikinsa, Manzon Allah yana daukan yatsansa sai ya dora a inda ciwon yake sannan ya karanta masa wannan addu'ar kamar haka:


"بِسْمِ اللَّهِ تُرْبَةُ أَرْضِنَا بِرِيقَةِ بَعْضِنَا يَشْفِي بِهُ مَقِيمَنَا بِإِذْ رَبَّنَا"


"Bismillahi turbati ardina bi riqati ba'adina, yashfa bihi thaqimuna, bi izni rabbina".


Yake 'yar uwa idan ki kayi wannan addu'ar kamar yadda Manzon Allah SAW yayi akan kowane irin ciwo ne, Allah zai yaye masa ciwon cikin dan kankanin lokaci Insha Allahu mu jarraba abun mu gani.


Yadda Ake Warkar Da Mara Lafiya Ta Hanyar Addu'a Kashi Na Biyu 2


Akwai hadisin Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Aishatu RA, tace; "Manzon Allah SAW in ya ziyarci wani cikin sahabbansa bashi da lafiya, yakan daura hannunsa ajikin mara lafiya ya karanta wannan addu'ar;


"اللَّهُمَّ رَبَّ النَّارِ أَذْهَبِ الْبَا وَأَنتَ الشَّافِي لأَشِفَاءَ إِلَّا شِفَاؤُكَ شِفَاءٌ لَا


يُغَارَ سَقَمًا"


"Allahumma rabbin nasi azhabal ba'asi wa antash shafi, la shifa'un illa shifa'uka, shifa'un la yugadiru


saqhan".


A karanta wannan addu'ar yayin da aka je duba mara lafiya. Allah zai raba shi da ciwo kowane irine cikin kankanen lokaci Insha Allahu.


Yadda Ake Warkar Da Mara Lafiya Ta Hanyar Addu'a Kashi Na Uku 3


Acikin sahihul Muslim an ruwaito daga Usman Ibn Abul Asi RA. Yazo gurin Manzon Allah SAW, yace akwai wani guri da yake masa ciwo a jikinsa. Sai annabi SAW yace: "Umar ce mashi ya rinka yin wannan addu'ar". Ga yadda yace dashi yace: ya dauki hannunsa ya dora a inda yake masa ciwon ya karanta sau uku;


" أَعُوذُ بِعَزَّةِ اللَّهِ وَ قُدْرَتِهِ مِنْ شَرَّ مَا أَجِدُ وَ أَحَاذِرُ".


"A'uzu bi izzatillahi wa qudratihi min sharri ma ajidu wa uhadiru"


Yadda Ake Warkar Da Mara Lafiya Ta Hanyar Addu'a Kashi Na Hudu 4


Daga bakin manzon Allah SAW. Acikin Sunnani Abu Darda'u da Nasa'i, an ruwaito daga Abu Zarri yace; Manzon Allah SAW yace "Idan wani mara lafiya yazo maku da ciwon daya tsananta a gareshi, to ku karanta masa wannan addu'ar:


رَبَّنَا اللَّهُ الَّذِي فِي السَّمَاءِ تَقَدَّ - اسْمُكَ أَمْرُ فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ كَمَا رَحْمَتُكَ فِي السَّمَاءِ فَاجْعَلْ فِي الْأَرْضِ فَاغْفِرْ لَنَا حَوْبَنَا وَ طَايَانَا أَتَ رَبُّ الطَّيبِينَ أَن فِي السَّمَاءِ فَاجْعَلْ رَحْمَةً مِّن رَّحْمَتِكَ وَشِفَاءُ مِنْ شِفَائِكَ فِي هذا الوجع فيبرا".


"Rabbanallahul ladhi fis sama'i taqdusu ismuka, amruka fissama'i wal ardi kama rahmatika fissama'i, faj'al fil ardi fagfir lana haubana wa khadayana anta rabbid dayyibin. Anzala fis sama'i faj'al rahmatan min rahmatika wa shifa'un min shifa'uka fi hazal waj'u fayabra".


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post