Yadda Ake Saka Laushin Hannu musamman ga mata
![]() |
Laushin Hannu |
Hanyoyin da ake amfani dasu don saka laushin fatar hannu ta yi kyau
Kullum bayan kin gama aiki, ki hada man zaitun da gishiri kadan ki rinka shafawa sau daya ko sau biyu a rana.
Ki hada sugar da butter dai-dai misali ki rinka murzawa a hannunki yayi tsawon misalin mintuna goma.
. Ki hada gilasirin (glycerin) da turaren miski da lemun zaki ki rinka shafawa a hannunki ko wane dare.
. Ki matsa ruwan lemun tsami da man zaitun ki rinka shafawa a hannunki, zai dawwama da taushi.
Ki samu tumatir kwaya bakwai ki matse ruwan ki hada da man zaitun cokali daya ki rinka shafawa kullum.
Da yawa daga cikin mata ba kowace mace bace tasan cewar idan ta gama wanke-wanke ta samu ruwan dumi ta wanke hannunta sannan ta shafe shi da mai. Duk matar da take hakan batada matsala ta fannin bushewar tafin hannunta. duk wanda cikin wadannan abubuwan da muka kawo, kika dauka zai miki amfani da yardar Allah
Leave Comments
Post a Comment