Yadda ake motso sha'awa yayin tabi |
A cikin kashi 100 kusan kashi 80 maza ne suke neman matansu idan aka zo batun jima’i, ina so mata su sani maza ba jin dadin hakan suke ba, sau da yawa nakan ji wadansu mazan na korafin hakan, sai dai idan sun bukaci matansu da batun jima’i ne suke amincewa.
Wasanni a yayin ko kafin Jima'i shine babban abinda ke haifar da jindadi da samun gamsuwa yayin Jima'i tsakanin ma'aurata. Ku yi kokarin a koda yaushe ku jiyar da Kanku dadi kafin ku yi jima’i.
Yin wasanni motsa sha'awa kafin Jima'i
Ba wai sai lokutan da za a sadu ba, ya kamata ku rika yi wa mijinku wasanni a wadansu lokutan da kuka lura yana cikin nishadi. Za ku iya masa wasannin ne ta hanyar shafarsa, sosa gashin kansa, tattaba yatsunsa da lankwasa su, inda wani lokaci za ku rika zungurarsa kadan. Yana da kyau ku rika ba shi labarai masu ban dariya da sanya nishadi, wani lokaci ku rika zolayarsa, yanayin yadda zai rika sake jikinsa gare ku zai nuna muku yana samun gamsuwa. Ta wannan hanyar ma za ku iya isar da sakon nuna son jima’i ba tare da bayyanawa da baki ba.
Neman jima’i bayan yin wasan tabi na sha'awa
A cikin kashi 100 kusan kashi 80 maza ne suke neman matansu idan aka zo batun jima’i, ina so mata su sani maza ba jin dadin hakan suke ba, sau da yawa nakan ji wadansu mazan na korafin hakan, sai dai idan sun bukaci matansu da batun jima’i ne suke amincewa. Maza suna so a ce matansu sun rika kirkiro hanyoyi daban-daban wajen isar da sakon son yayin jima’i, a lokuta da dama mata suna zama ne kawai ko da kuwa suna son jima’i, amma sai su yi gum har sai mijinsu ya bukaci hakan, wannan takan sanya namiji ya rika tunanin shi ne kawai yake son saduwa, sannan matansa babu ruwansu, hakan zai sa ya kasa samun ingantacciyar gamsuwa, ina so mata su fahimta ba wai zubar da maniyyi yana nufin gamsuwa yayin jima’i ba, a’a, samun gamsuwa a zuciya shi ne babbar gamsuwa.
Kalaman soyayya a lokacin jima'i
Za ku iya kara wa jima’i armashi idan kuka rika yi wa mijinku kalaman soyayya, ko ku rika yi masa kirari, hakan zai sa ya rika jin dadi, inda kafin a ce wani abu ma sai ku ji ya samu gamsuwa, domin ita zuciya Allah Ya halicce ta da son kalaman da za su dadada mata, ta hanyar yi wa mijinku kalaman soyayya lokacin jima’i sai ku kara tasirantuwa a zuciyarsa har ya ji kun gamsar da shi ba tare da shan wahala ba. Kada ku yi zaton hakan kaskantar da kai ne, ba haka ba ne, yin wadannan kalaman zai sa mijinku ya rika jin kamar shi ne kadai namiji da ya rage a duniya.
Yin Tausa a lokaci ko bayan Jima'i
Bayan mijinku ya kai ga zubar da maniyyi wani abu da za ku yi masa don ya samu cikakkiyar gamsuwa shi ne, ku kankame shi a kirjinku zuwa wani dan lokaci, sannan ku rika yi masa tausassan kalamai a kunnensa, lokaci zuwa lokaci ki rika wasa a harshenki a kunnensa, a lokaci guda ki rika yi masa rada a kunnensa. Daga bisani ku rika yi masa tausa, za ku yi masa tausa ne a gabobinsa da kuma wuraren da suke motsa sha’awa. A yayin tausar za ku iya amfani da yatsunku ko harshenku wajen yin wasa a kwarin bayansa, kwarin dunduniyarsa da wuyansa da kuma kwarmin bayan kunnensa, wannan yana sanya maza nishadi da sakewa bayan an yi jima’i, hakan kuma zai ba shi cikakkiyar gamsuwa.
Ba jima’i muhimmanci
Wadansu matan suka nuna halin ko in kula a lokacin jima’i, to hakan na nakasa karsashin namiji wajen samun gamsuwa, kada ku nuna wa mijinku tamkar taimakonsa kuke yi yayin jima’i, Ku sadaukar da kanku, ku bayyana zautuwarku a lokacin da yake saduwa da ku, hakan zai ba shi gamsuwa ta hakika.
Bayyana sirri
Yana da matukar muhimmanci ku bayyana wa maigidanku sirrinku a bangaren jima’i, domin ta haka ne zai samu wani makulli da zai rika bude muku sha’awa har ya kai ga gamsar da ku, inda hakan ne zai ba shi damar samun cikakkiyar gamsuwa.
zan yi muku bayanin wadannan wurare tara don su kasance wani sirri a wurinku da za ku rika sarrafa mazajensu yayin jima’i cikin ruwan sanyi.
Wadannan wurare suna dauke da jijiyoyi wadanda kai tsaye suke aika sako zuwa kwakwalwa cikin kankanen lokaci. Wadannan wurare sun hada da:
1. Cikin leben kasan baki
Bakin namiji wuri ne da ke saurin aika sako zuwa kwakwalwa, kuma ga namiji yana saurin motsa masa sha’awa. Ba wai na sanar da ku wannan wurin sai kuma ku rika nacewa wajen tsotsar leben mijinku ba, hakan zai sanya ya ji kun gundure shi, lokaci zuwa lokaci za ku rika tsotsar wajen kasan lebe.
A jikin lebe akwai wadansu kananan jijiyoyi wadanda suke motsa sha’awa cikin kankanen lokaci.
Yadda za ku yi: A lokacin da kuke son motso da sha’awar mijinku, sai ku tura leben kasan bakin mijinku cikin bakinku, sannan ku rika amfani da ita.
Yadda za ku yi: A lokacin da kuke son motso da sha’awar mijinku, sai ku tura leben kasan bakin mijinku cikin bakinku, sannan ku rika amfani da tsinin harshenku kuna wasa da shi a kan fatar leben mai dauke da tarin kananan jijiyoyi masu isar da sako ga kwakwalwa. Za ku ci gaba da zuwa da dawowa da harshenku, inda hakan zai sanya mijinku ya tafi wata duniya cikin jin dadi. Zai rika jin kamar ana yi masa susa mai dadi a bakinsa ne.
Wani abu da nake so in ja hankalinku shi ne, ku rika kula da bakinku, ma’ana ku tsaftace shi ta hanyar goge bakinku sau biyu ko uku a rana, ko kuma daf da lokacin da kuke so ku sumbaci mijinku don kada ya rika jin kyamarku, idan har kuna so tsotsar lebe ya kara armashi, to za ku iya sanya minti mai zaki a bakinku, walau lokacin da kuke tsotson ko kuma kafin, hakan zai sanya yawun bakinku ya kasance cikin zaki da kuma kamshin mintin.
2. Gaban Wuya
Yawancin mata ba su da masaniyar cewa wuya na motsa sha’awar namiji, wadanda suka sani kuma sun fi mayar da hankali wajen shafa gefen wuya ne, amma a zahirin gaskiya wurin da ya fi motsa wa namiji sha’awa a wuya shi ne gaban wayansa daidai saitin makogwaro, domin akwai kororon da ya wuce har zuwa cikin ciki, kuma wannan kororon yana dauke da jijiyoyin kanana da kai tsaye suke tura sako ga kwakwalwa, sannan suna taka muhimmiyar rawa wajen motsa sha’awar namiji. Wani masanin magani dan kasar China mai suna Mantak Chia, ya bayyana makogwaro yana dauke da jijiyoyin da suke da kusanci da gabobin sha’awa.
Yadda za ku yi: Ku kwantar da mijinku a kan filo kamar yadda kuke kwantar da jariri, wato ya kwanta da bayansa kansa ya kalli sama, hakan zai ba ku damar ganin ko’ina a wuyansa. Daga nan ku yi amfani da harshenku wajen lashe wuyansa, musamman ma kan makogwaronsa, daga nan ku ci gaba da wasa da harshenku a wuyansa har zuwa daidai habarsa. Za ku iya amfani da hannunku wajen yi wa wuyan tausa, musamman ga namijin da yake da bayyanannun jijiyoyi a wuyansa ko kuma makogwaron wuya.
3. Cibiya
Cibiya wani wuri ne na matattarar sha’awar dan Adam, amma mata ba su cika mayar da hankali wajen amfani da ita wajen sosa ran mijinsu ba.
Yadda za ku yi: A wannan lokacin ma za ku kwantar da mijinku a kan matashin kai, kansa ya kalli sama, sannan ku yi amfani da yatsunku wajen sosa masa cibiya, ko ku rika zagaya shatin cibiyar da yatsunku. Wani salo da za ku yi amfani da shi ne, amfani da harshenku wajen lashe cibiyar, sannan idan mijinku yana da kwarin cibiya, za ku iya zuba yawunku a cikin sannan ku rika kada harshenku a ciki, za ku ga yadda zai rika numfarfashi da gurnani. Idan kun jika cibiyarsa da yawunku, za ku rika hurawa, iskar da za ta sauka a cibiyar za ta sa sha’awar mijinku ta motsa. Sannan za ku iya tsotsar cibiyar ko sosa ta da hakoranku. Za ku kuma iya cizonta amma ba da karfi ba.
Wata hanya da za ku bi wajen kara rikitar da mijinku shi ne, za ku iya shan kankarar ice cream, ko ruwa mai sanyi, hakan zai sanya harshenku ya dauki sanyi, idan kuka dora harshenku a kan cibiyar mijinku zai ji kamar ana bibration a cibiyarsa, har bai san lokacin da zai rungume ki a jikinsa ba.
Illar rashin yin tsafta da kwalliya ga mata
A kodayaushe ina jin dadin yadda idan na rubuta mukala nake samun wayoyin mutane daga garuruwa daban-daban yadda kowa ke bayyana min jin dadinsa da kuma addu’o’i na alheri sannan da yadda ake nuna min ana amfana da abin. Wannan shi ke rara min kwarin gwiwa wajen sako rubuto abin da zai amfane mu baki daya a duk lokacin da na samu dama.
Akwai masu ba ni shawarwarin a kan a duk lokacin da na yi rubutu a kan wani fanni to in rika daurewa ina ci gaba saboda yana yi musu dadi kuma suna amfana. Amma a ganina da in dauki fanni daya in ta yin rubutu a kansa, to gara in dauko wani fannin da shi ma za mu karu da shi.
Na san wasu za su ce me ya sa a kullum rubutuna ya fi rinjaye ne a kan mata? Dalilin da ya sa na fi karkata a kan mata shi ne kasancewata ’ya mace kuma in a kishin na ga mace ko mata ’yan uwana suna cikin wani yanayi da ke bukatar a wayar musu da kai don su gyara. Ba don komai na fi karkata a kanmu mu mata ba sai don ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, don ina kishin in ga ‘yar uwata mace a wani hali, kuma a cikin zamantakewa ta aure dole mata mu ne a kasa seai mun fara gyara wa sannan abubuwa za su inganta a zamantakewar baki daya, don wasu matsalolin da yawa daga garemu ne, amma su ma mazan da nasu, amma fannin da na dauko yau na tsafta da kwalliya kusan ya shafi kowa da kowa ne watau daga matan har mazan domin ita tsafta ko don lafiyar jikinmu yakamata mu tsaya mu lura da ita. Allah Ya datar da mu baki daya.
Tsafta cikon addini ce, tsafta tana daga cikin imani, kazanta wata abace da take taka muhimmiyar rawa a wurin wargaza zamantakewa musamman ta aure, domin kazanta ba karamin ragewa mace kima takeyi a idon mijinta ba kuma sh ima mijin tana rage masa tasa kimar a idon matarsa, don kazanta tana haifar da kiyayya a zamantakewa.
Akwai abubuwan da yakamata mu lura da su, mu inganta su a wurin gina tsaftarmu. Misali wanka, wanki, wanke kai, goge dattin kunnuwa, wanke baki, wanke hannu, yankan farce, da sauransu.
Manzon Allah (SAW) yana cewa Allah Mai tsarki ne kuma Yana son tsarkaka. Idan mun duba za mu ga addinin musulunci kansa an gina shi ne a kan tsafta saboda fadin Manzonmu (SAW) cewa an gina musulunci ne a kan tsafta kuma babu mai shiga aljanna sai me tsafta. Hadisai da yawa sun yi nuni a kan bayanin muhimmancin tsafta kuma sun yi nuni da kyamar da Allah (SWT) Yake yi wa mai rashin kula da tsafta.
Jiki yana bukatar tsafta, ko na mutum ko na dabba, don rai ta sami sukuni. Wannan yana nufin ba za a samu tunani mai kyau tare da kazami ba.
A nan ina so mata su gane cewa muna da daraja da kima dole sai mun tsaya mun lura da abubuwa a cikin zamantakewar aure sannan gidanmu zai gyaru, mu kwato wa kawunanmu ‘yancinmu a hannunmu domin addinin musulunci ya fi kowane addini tausaya wa mace a tarihin dan adam.
Amma abin da ke ban mamaki sai ka shiga gidan mace ka ganshi kaca-kaca, babu sha’awa, kazanta ta tare tun daga tsakar gidanta da dakunanta da ban-daki har ita kanta. Ga tulin kayan wanki da wanke- wanke kuda suna bi ko kayan wanki a jibge, yara kuwa sai ka gan su dukun-dukun, hanci dagaje- dagaje da majina. Idan ma girki take yi sai ka gan shi a bude ko an bude murfi an bar shi a kasa ana face majina, wannan yana daga cikin abin da maza suka tsana. Kuma koma wane ne ransa ba zai so ba. Shin ‘yar uwa ba ki san kina dasa kiyayyarki a zuciyar mijinki ba? Duk kuwa da irin soyyayar da kike ganin yana yi miki?
Wasu matan ba su dauki kwalliya da muhimmanci ba shi ya sa wasu mazan suke burin kara aure ba don ya fita ya bar ki dukun-kudun cikin dauda da tsami amma a lokacin da ya fita sai ya hadu da wata tsaleliyar budurwa tana karairaya ga shi ta caba kwalliya tana kanshi me kike tunanin zai faru, tilas ya fara saka wa a zuciyarsa zai kara aure.
Abun lura a nan shi ne, ban ce su mazan ba su da laifi ba, don a wasu lokutan za ka tarar matan ne ke da tsafta amma maigida ya kasance cikin wani irin mummunan yanayi saboda rashin tsafta. Amma dai abin da nake so mu lura da shi a nan mu mata mu gida ke hannunmu, duk yadda muka so sarrafa maza haka za su bi mu kamar akalar rakumi.
Duk macen da ta iya taku, ta iya kwalliya, ta iya girki, ta iya gyara gidanta ciki da waje, babu shakka za ta samun kan mijinta cikin sauki. Da zarar ya shiga gidan, ba zai yi marmarin fita ba in ba tare da wani kwawwaran dalili ba, don yana jin dadin zama a ciki. Ga shi gidansa ya yi fes-fes, ga uwargida ta caba kwalliya, don haka zai ji tamkar yana aljannar duniya ne.
Amma idan mace ta kasance cikin dauda, gidanta da dakinta dikin dauda, da zarar miji ya dawo to zai yi Allah-Alah ne ya bar gidan,. Wasu ba za su sake waiwayar gidan ba sai cikin tsakar dare lokacin kwanciya, kuma da zarar gari ya waye za ka ga suna hanzarin barin gidan, don wasu ko karyawa ma ba za su iya yi a cikin gidan ba saboda kazanta, sun gwammace su tafi teburin mai shayi ko dakunan cin abinci, su karya a can.
To irin wannan da me ya yi kama? Yakamama mata mu yi wa kanmu fada, mu sani igiyar aurenmu a hannunmu take, sai yadda muka so juyawa da ita. Don haka ya dace mu yi karatun ta-natsu, don mu samu zaman lafiya mai dorewa a gidajen aurenmu.
Da fatan za mu kiyaye, Allah Ya taimake mu.