Yadda Ake Maganin Kurajen Fuska( pimples)
Yadda Ake Maganin Kurajen Fuska( pimples) |
Yadda ake yin maganin kurajen fuska musamman ga mata
Ina matan dake fama da matsalar fesowar kuraje musamman a fuska, ga tsaraba na kawo muku yadda ake magance kurajen fuska.
Yawancin yan mata ne ake samu da fitowar kuraje a fuska galibi farkon balaga. Don yawanci an fi samun mata daga shekara 14 zuwa 20 da kuraje ke fito musu a fuska.
Don kawar da kuraje, ku samu wadannan abubuwa kamar haka;
- Man Habbatussauda cokali 1
- Man tea tree
- Garin Masara cokali 1
Yadda Ake Hadawa
A samu man habbatus sauda mai laushi cokali É—aya a gaurayi shi a cikin man tea tree, tare da garin masara cokali É—aya kullum, sai a shafe shi gabaÉ—aya a fuska ta hanyar lullube fuskar baki daya na tsawon awa É—aya sannan a wanke da ruwan dumi da sabulu, sannan kuma a maimaita haka har tsawon sati daya.
Yana da kyau idan kika kara da shan man habbatus sauda a cikin ruwan dumi.
Allah ya baiwa duk wasu marasa lafiya, Lafiya
Bashir Suraj Adam
Leave Comments
Post a Comment