Yadda Ake Hadin Karin Ni'ima (Sa Kishiya Tagumi) |
Hanyoyin karin niima musamman ga amare har da uwargida
Yau na kawo muku hanyoyin da za ku yi amfani dasu don samun karin ni'ima musamman ga matan aure. Wannan hadin yana sauko wa mace ni'ima. Maigida zaiji baya gajiya da kai miki ziyara.
- Kwakwa
- Garin dabino
- Madara peak
Yadda ake hada karin niima (sa Kishiya Tagumi)
Ki markada kwakwa da dabino ki tace, sai ki zuba madarar peak ki rinka sha. Zakiga abin mamaki Insha Allah.
Hadin Kaza Na Karin Ni'ima
Wannan hadin na mata da maza ne. Yana sanya ma'aurata farin ciki a duk lokacin da suka sadu da juna. Ki samu wannan kayan hadin;
- Kaza
- Saiwar malmo
Yadda ake hadin karin niima da kaza:
Zaki samu saiwar malmo ki dafa shi, sai ki tace ruwan. Ki samu kázarki ki gyara ita, ki hada mata komai na dahuwa. Sai ki zuba ruwan dahuwar malmon da kika tace. A jaraba za'aga biyan bukata da yardar Allah.
Hadin Danyar Gyada Na Kara Ni'ima
Wannan hadin yana sanya maigida ya kasance a dakinki koda yaushe. Idan ma kinada kishiya har sai ta rasa me yake idan ya shigo dakin naki.
Ki samu danyar gyada ki wanke ta, sai ki jika ta ki kai a markada maki ki tace, kya iya zuba sugar ko zuma sai ki saka a fridge, domin gudun lalacewa. In zaki kwanta kisha karamin kofi, ki sha mamaki.
Hadin Niima Na Manta Wayarka
Wannan hadin shima yanada matukar amfani ga jikim mace. Ki samu;
- Ruwan rake
- Rüwan kankana
- Madara
Yadda ake hadawa
Ki hadasu waje guda ki motse ki rinka sha sau uku a rana. Ki jaraba don akwai amfani a cikin wannan hadin.
Hadin Niima Na Makale Mata
Wannan hadin shi ake kira da 'makale mata' Zaki samu wannan abubuwan kamar haka;
- Aya
- Waken suya
- Kwakwa
- Dabino
- Madarar ruwa
- Zuma
Yadda ake hadawa:
Ki hadesu guri guda ki markade, sai ki tace ki zuba zuma da madarar ruwa ki rinka sha. Keda kanki zakiji canji tun daga lokacin da kika fara sha.
Wannan Hadin Yana Karawa Mace Niima Da Dadi
- Garin aya gwangwani biyu 2
- Garin dakakkiyar kwakwa gwangwani biyu 2
- Garin dabino gwangwani biyu 2
- Madarar ruwa
- Zuma
Yadda ake hadawa:
Ki hadasu guri guda ki rinka diba kina zubawa cikin madara kina zuba zuma, ki rinka sha. Wannan hadin yana matukar ruda maigida yana kuma sauko da ni'ima cikin sauri.
Karin Ni'ima na musamman
Shima wannan wani hadin Karin Ni'ima ne na musamman, samu;
- Gujjiya
- Murucci
Yadda ake hadawa:
A shanya su su bushe sai a daka su zama gari. A rinka diba ana sha da madara. Wannan hadin mace da namiji zasu iya amfanı dashi domin jin dadin su.
Hadin Niima (Dan Bashanana)
Wannan hadin yana sanya gaban mace ya ciko, naman gurin ya ciko Koda irin matan nan ne wadanda gabansu yakeda zurfi. Zaki samu:
- Nama
- Nonon akuya
Yadda ake hadawa:
Ki samu namanki ki gyara shi ki dafa, ki hada masa kayan hadin farfesu. Idan ya dauko dahuwa sai ki kawo nonon akuyarki ki zuba aciki. Ki barshi yayi dan mintoci sai ki cinye. Wannan hadin shima fa ba magana, sai an jaraba sannan ake sanin na kwarai.
Hadin Niima ko Tsumin 'Yar Gata
Shima wannan hadin Niima ne dake da tasiri a jikin mace, ki samu
- Dabino kwano biyu 2
- Mazarkwaila kofi biyu 2
- Bawon kankana
- Dakakken kanunfari
Yadda ake hadawa:
Ki cire kwallayen dabino sai ki jika dabinon yayi kaushi, sannan ki tace ruwan dadinon ki kai a markada maki. Sai ki dafa bawon kankana, idan ta tafasa sosai, ki zuba mazarkwaila aciki da dakakken kanunfari. Sai ki mayar akan wuta har sai yayi kauri sai ki kwashe. Idan ya huce sai ki rinka sha cokali uku sau uku a rana. Zaki sha mamaki.
Hadin Niima na 'Yar Lelen Maigida
Wannan hadin yana sanyawa uwargida tazama 'yar lele agun maigidanta. Ki samu wannan abubuwan;
- Aya
- Gyada
- Dabino
- Mazarkwaila
- Dankalin hausa
Yadda ake hadawa:
Zaki gyara dankalinki na hausa ki yanka kanana. sai ki shanya shi ya bushe sai ki zuba masa kayan kamshi kadan ki daka Sannan ki dauko dabino da mazarkwaila ki soya gydar ki, amma kada ta soyu sosai, sai ki hada Dabino da mazwaila ki dakasu, ki fitar da bawon madara. Wannan hadin zaki yaba.