Yadda Ake Hadin Karin Kugu (hip)
![]() |
Yadda Ake Hadin Karin Kugu (hip) |
Yadda ake yin maganin karin kiba, maganin tabo ajiki da magance kurajen fuska
Macen da take bukatar kugu, ko take da matsalar rashin yalwar kugu bayan nata ya zamanto a shafe. Sai ta samu wadannan kayan lambun;
- Abarba
- Ayaba
- Gwanda
- Kankana
- Zuma
- Madara peak
Ki hadasu guri guda ki markada su sai sun zama ruwa, sai ki zuba zuma da madara ki rinka sha. Sai kuma ki samu zogale dafaffe ki hada da alayyahu da tumatir ki zuba albasa kiyi kwadon su. Haka zaki rinka yi ga kwadon, ki rinka yin wadannan kayan lambun da kika markada sai ki rinka sha safe da yamma. Insha Allahu za'a dace.
- Maganin Kaushi
- Spirit
- Hydrogen murfi biyu 2
- Man kadanya
- Ganyen magarya
Sai ki hadesu a cikin mazubi daya ki rinka shafawa a kafarki kafin ki shiga wanka da misalin mintuna ashirin. Sai kiyi amfani da sabulu ki wanke kafarki fes, zaki sha mamaki.
Maganin Tabo A Jiki
Ki samu khal babban cokali daya, sai ki hada da ruwa kofi biyu ki tafasa. Bayan ya huce sai ki rinka shafawa ajikinki. Insha Allah kinyi bankwana da duk wani tabo dake jikınki.
Maganin Tabo A Fuska (MUDDIN BAI RASA FATA BA)
- Lemun tsami
- Man dalbejiya
- Man zogale
- Farar wuta kadan
Ki zuba farar wutar kadan saboda tanada zafi, ki hadesu guri guda sai ki rinka dangwala ki cudanya kina gogawa a gurin tabon. Insha Allahu tabon zai goge.
Maganin Kuraje A Jiki
A samu garin zogale da man zaitun, sai a hadesu guri guda a rinka shafawa.
Kula Da Tafin Hannuwa
Laushin tafin hannu ga mace yanada mahimmanci sosai, kamar yadda bushewarsa yake tattare da matsala. Ko kinsan ta ni'imar tafin hannun mace masana ke gane mace ko wace iri ce? Kamar yadda Allah SWT ya halicci kowace halitta da abinda ke tattare da wannan halitta, to haka kowacce akwai baiwar da Allah ya bata. Sai dai wata nata yafi na wata. Amma idan kina son wannan ni'imar da Allah ya halicce ki da ita ta dawwama to dole ne kiyi tattalinta, don kada ta gushe. Dole ki samu matsala gurin gamsar da maigida.
Masana wannan fannin suna kallon tafin hannunki sun gama gane ko ke wacece. Don haka kada ki dogara ga mai mai sanya taushin fata na hannu, wato hand lotion, baya aiki face na mintoci kadan.
Leave Comments
Post a Comment