Yadda ake Gyaran Jiki Na Musamman - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yadda ake Gyaran Jiki Na Musamman

Yadda ake Gyaran Jiki Na Musamman
Yadda ake Gyaran Jiki Na Musamman 


 Hanyoyin gyaran jiki na musamman ga mata da masu shirin yin aure 


Gyaran jikin mace yanada matukar muhimmanci a tare da ita. 'Yar uwa kada ki bari fatar jikinki ta koma tamkar ta wata tsohuwa, anaso koda wane lokaci fatarki ta kasance tanada kyau tana kuma sheki. Haka ma zai sanya koda wane lokaci mijinki yana son kasancewa tare dake, kuma ko fita yayi waje babu fatar wata 'ya mace da zai kalla ta dauke masa hankali, saboda yasan ta gidansa a gyare take a koda wane lokaci.


Gyaran Jiki Na Daya (TANGARAN)

Wannan hadin gyaran jiki ne dake gyara fata da laushi fata. Ki samu;

  • Ganyen dalbejiya
  • Lalle
  • Zuma
  • Zaitu Laus
  • Sabulun gana
  • Dudu Osun

Ki hadasu guri daya ki daka a cikin turmi mai tsafta, sai ki rinka wanka dashi, Zaki ga yanda fatar jikinki zata canza.


Gyaran Jiki Na Biyu (MAI TASA)

Wannan hadin yana saka hasken fata da shekin fata, ki samu;

  • Sabulun salo
  • Sabulun gana
  • Lemun tsami
  • Kurkur
  • Kanunfari
  • Kwai

Sai ki hadasu guri guda ki rinka wanka dasu. Shima wannan hadin yana gyara jiki, fata ta rinka sheki da sulbi.


Gyaran Jiki Na Uku (HAKA NA KOMA)

Shima wannan hadin yana da kyau sosai domin yana gyara jiki, samu 

  • Man ridi
  • Man kwakwa
  • Man habbatus sauda
  • Zaitu laus

Ki hada su guri guda ki rinka shafawa. Wannan hadin yana sanya fatar mace tayi laushi tayi santsi yanda maigida bazai gaji da tabawa ba.


Gyaran Jiki Na Hudu (AKORI BLEACHING)

Ki samu bawon lemun zaki ki shanya ya bushe, sai ki daka shi ki kwaba da ruwa, ki rinka shafawa a fuskarki da sauran sassa na jikinki. Zuwa misalin mintina talatin sai ki shiga wanka. In kin fito sai ki shafa man hulba da na ridi.


Gyaran Jiki Na Biyar (KINFI AMARYA)

Shi wannan hadin yana gyara jiki sosai domin jiki zai kara kyau. Ki samu 

Albabunaj.

Ki kwaba shi da ruwan kwai ki shafe jikinki dashi. Wannan hadin yana matukar gyara jikin mace. Bayan kin wanke zaki iya shafa kowane kalar mai da kike amfani dashi.


Gyaran Jiki Na Shida (AMININ MATA)

Yana gyara fatar jiki sosai, ki samu 

  • Garin alkama
  • Zuma
  • Madara peak

Ki hada su guri guda ki cakuda ki rinka shafawa. Kafin ki shiga wanka ki rinka yin hakan, zaki ga abun mamaki.


Gyaran Jiki Na Bakwai (MAI TAS)

Shima wannan gyaran jiki ne na musamman dake sa laushin fata

  • Sabulun salo
  • Farar albasa
  • Garin lalle
  • Garin zogale
  • Madara/kwai
  • Kurkur

Da farko zaki tanadi sabulun salo mai kyau, sai ki nemi farar albasa itama mai kyau guda daya, sannan ki jajjagata tayi laiushi sosai yadda idan kin sakata acikin sabulun zata bi shi. Ki samu wani sabulun daban irin wanda kike wanka dashi sai ki kirba su guri guda, ki zuba farar albasa ki cigaba da dakasu har sai ya daku. Ta yadda in zakiyi amfani dashi sai ki zuba madarar, lalle, garin zogale, kurkur ki mulmula, ki rinka wanka dashi zakiga canji.


Gyaran Jiki Na Takwas (MAI AUDUGA)

Wannan hadin yana sa fata ta gyaru ta yi laushi. 

  • Kwai guda daya 1
  • Lalle cokali daya 1
  • Gishiri rabin cokali 2
  • Kurkur cokali daya 1
  • Manja cokali uku 3

Sai ki hadesu guri guda ki cakuda su gaba daya, ki rinka shafawa da daddare idan zaki kwanta bacci, da safe sai ki wanke. Zakiga yadda fatarki zata goge ta rinka sheki, tana fitar da wani haske na musamman da annuri. Ki jarraba ki gani.


Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel