Gyaran Fuska Da Zuma |
Zuma wani samfurin halitta ne da zai iya amfanar fata, musamman idan aka yi amfani da ita a matsayin maganin fuska. Ansan amfani da zuma yana da yawa musamman don rigakafin kwayoyin cuta da warkar da fata da gyara fuska
Ana yin amfani da magunguna irir-iri don gyara fuska da kara hasken fata a fuska. Mata da dama suna kashe Kudaden su wajen siya da hade-Haden sinadarai don gyara fuska. Wanda wasu daga cikin sinadaran ke tasiri wajen lalata fatar jiki. Hakan yasa na kawo muku yadda za ku yi gyaran fuska da zuma, cikin sauki ba tare da yin amfani da wasu sinadarai da kan iya barazana ga lafiyar fatar ku.
Zuma wani samfurin halitta ne da zai iya amfanar fata, musamman idan aka yi amfani da ita a matsayin maganin fuska. Ansan amfani da zuma yana da yawa musamman don rigakafin kwayoyin cuta da warkar da fata da gyara fuska. Ga wasu hanyoyin da za a iya amfani da zuma don gyara fuska:
Gyaran Fuska Da Zuma
Amfanin da zuma don gyara fuska yana taimakawa fata ta yi kyau, haske, laushi.
1) Laushin Fata: Shafa zuma kai tsaye a fuska a bar shi na kimanin minti 20 kafin a wanke. Wannan zai iya taimakawa wajen saka laushin fata. Matan dake son fuskar su ta kasance mai laushi da sulbi, ku dinga shafa zuma a fuska akai-akai za ku yi mamakin yadda fuska za ta yi.
2) Magance Kuraje: Saboda saindarai masu inganci dake cikin zuma da yin rigakafin kwayoyin cuta, ana iya shafa zuma a wuraren da kuraje ke fitowa a fuska don taimakawa rage fesowar kuraje warkar dasu. A takaice ana iya shafa zuma a fuska don magance kowane irin kurji dake fitowa a kan fuska.
3) Rage Tabo: Aikace-aikacen zuma na yau da kullun akan tabo na iya taimakawa wajen rage su ta hanyar inganta sabunta fata. Matan dake da tabo a fuska a dalilin fitowar kuraje, suna iya gyaran fuska da zuma, ku dinga shafawa na dan lokaci sannan ku wanke fuskar. Yin hakan yana magance dukkan tabo dake fuska.
4) Gyara Fuska; Zuma na iya aiki a matsayin mai irin wanda mata ke amfani dashi don fuska tai kyau. Shafa zuma a fuska yana cire sel din fata da suka mutu kuma yana sa fata ta yi haske ta yi fresh.
Gyaran fuska da zuma, yana da yawa kuma duk wanda suke yin amfani da zuma a fuska sun san muhimmancin aikin da take yi. Sai dai yana da muhimmanci a yi amfani da zuma mara sarrafawa, mara tacewa don tabbatar da cewa an adana kaddarorin masu amfani. Musamman ana bada shawarar zuma na asali wacce ba'a yiwa hade-hade ba.