Yadda Ake Addu'ar Neman Tsari |
Addu'ar Neman Tsari
Yau a wannan topic na kawo muku yadda ake yin addu'ar neman tsari, da fatan Allah ya amshi ibadun mu ya tsare mu daga dukkan wani sharri.
1. Addu'ar Neman Tsari
Wani mutum yazo gurin Abu Darda'i (RA) sai yace dashi; " ya Abu Darda'i hakika gidanka ya kone"
Sai Abu Darda'i yace: "A'a gidana ba zai kone ba, don nasan Allah ba zai karya alkawarinsa ba, na duk wanda ya fadi wasu kalmomi da naji annabi (SAW) yace duk wanda ya fadesu a wannan yini to babu wata masifa da zata same shi. Niko nasan na fadesu a yau, tashi muje mugani". Sai suka isa gidan babu abinda yasamu gidan. To wadannan kalmomi da annabi (SAW) ya fada sune kamar haka:
اللهُم أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إِلا أَنْتَ إِلَيْكَ تَوَكَّلْتُ وَأَنْتَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ مَا شَاء اللَّهُ كَانَ وَمَا لَمْ يَشَأْ لَمْ يَكُنْ لاحَوْلَ وَلا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ الْعَلَيَّ العظيم. واعْلَمُ أَنَّ اللَّهَ عَلَى كُلَّ شَيْءٍ قَدِيرٌ وَ أَنَّ اللهَ قَدْ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيْءٍ عِلْمًا. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِنْ شَرَّ نَفْسِي وَ مِن شَرَّ كُلِّ دَابَّةٍ أَنْتَ آخِذْ رَبِنَاصِيَتَهَا, وَ أَنَّ
ربي عَلَى صِرَاطِ الْمُسْتَقِيمِ"
"Allahumma anta rabbi la'ilaha illa anta, alaika tawakkaltu wa anta rabbul arshil azim. Masha allahu kana wama lam yasha'a lamyakun. La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim. Wa'alam annallaha ala kulli shai'in qadir wa annallaha qad ahada bikulli shai'in ilma. Allahumma inni a'uzubika min sharri nafsi, wamin sharri kulli dabatin anta akhizun binasiyatiha, wa anna rabbi-ala siradil mustaqeem".
2. Addu'ar Neman Tsari II
Anaso duk wayewar gari mutum ya karanta wannan addu'ar koda sau daya a rana ne. Mazaunin gidane, kokuma matafiyi. Don neman tsari a wajen Allah, yabaka kariya dakai da iyalenka daga sharrin mutane da aljanu.
Malamai sunce, koda zaka bar gidanka a bude Allah bazai bari wani wanda zai cutar dakai ko kuma ya cutar da iyalenka ya shiga gidan ba. Kuma Allah zai baka kariya daga sharrin makota masu cin amana. Makotansu su nemar masu mata ko kuma su lalata masu 'ya'ya.
Zakayi tafiya kaje kadawo hankalinka kwance da yardar Allah. Ga addu'ar kamar haka; ku haddaceta kusa yaranku su iya suma.
" اللَّهُم إِنِّي أَعُوذُبِكَ مِن سَاعَةِ السَّوْءِ وَ يَوْمَ السَّوء, و ليلة السوء و صديق السوء, وَ جَارِ السُّوْءِ, وَأَعُوذُبِكَ مِن ذِي الْوَجْهَيْنِ وَ ذِي النِّسَانِينِ. وَ أَعُوذُبِكَ مِنْ إِبْلِيسَ وَ أَعُوذُبِكَ مِن سَاعَةِ الْغَفْلَةِ, رَبَّنَا عَلَيْكَ تَوَكَّلْنَا وَأَنْتَ رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ. اللَّهُمَّ إِنِّي حَصَّنْتُ نَفْسِي وَ أَهْلَ بَيْتِي جَمِيعًا بِالْحَيِّ الْقَيُّومُ الَّذِي لا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلا نفو"
"Allahumma inni a'uzubika min sa'atis su'i, wa yaumis su'i, wa lailatus su'i, wa sadiqis su'i, wa jaris su'i, wa a'uzubika manzil wajhain wazil lisanain, wa a'uzubika min iblis, wa a'uzubika min sa'atil gafla. Rabbana alaika tawakkalna wa anta rabbul arshil azeem. Allahumma inni hassantu nafsi wa ahli baiti jami'an bil hayyil qayyumil lathi la ta'khuzuhu sinatun wala naum"