Yadda Ake Addu'ar Neman Tsari Νa Κai Da Iyali Daga Annoba |
Addu'ar Neman Tsari Νa Κai Da Iyali Daga Annoba
Wannan addu'ar anaso kayita ko kiyita dan neman tsari daga wajen ubangiji kai da iyalenka. Wannan addu'ar tanada matukar muhimmanci.
Anaso da safe kafin ki kama harkokin gida ko kafin ka fita kasuwa, kiyi salatud-duha (sallar da ake yinta in rana ta fito, kamar karfe 9:00 ko 10:00), tanada matukar muhimmanci. A wani hadisin Qudsi Allah SWT yace, "Bayina kuyi min raka'ah hudu a farkon rana ni kuma na zama gatanku, har dare ba mai tabaku".
Sannan Abu Hurairah RA yace;' Masoyina Annabi Muhammad SAW, yayi min wasilci da abubuwa uku (3) masu mahimmanci. Na farko salatud-duha raka'ah hudu duk farkon rana. Na biyu azumi luku duk farkon wata, Sannan na uku, banyi bacci ba sai nayi shafa'i da wutiri'.
Wadannan abubuwan in kasaba dasu rayuwarka zaka sha mamaki. Ko sihiri bazai tasiri awajen kaba bare aljanu ko kambun baka. Anaso bayan kinyi raka'ah hudu kinyi sallama sai ki karanta wannan addu'ar kamar haka;
"اللَّهُمَّ لَا تَرْفَعُ عَنَّا غِطَاءُ سِتْرِكَ وَلَا تَبْتَلِينَا فيما لا نَسْتَطِيعُ عَلَيْهِ صبرا. اللَّهُمَّ أَسْأَلُكَ رَاحَةً فِي الْبَدْنِ وَرَاحَةً فِي الْقَلْبِ وَرَاحَةً فِي النَّفْسَ وَبَارِكْ لَنا فِي عُمُورِنَا وَصِحَتِنَا وَ أَوْلَادِنَا وَاحَسِنْ خَوَاتِمَنَا وَلَا تَتَوَفَّنَا إِلَّا وَأَنْتَ رَاضِيًا عنا
"Allahumma la tarfa'a anna gida'a sitrak, wala tabtalina fima la nastadi'u alaihi sabra, allahumma as'aluka rahata fil badan, wa rahata fil qalb, wa rahata fin nafs, wa barik lana fi umurina wa sihhatina wa awladina, wahsun khawatima na wala tatawaffana illa anta radiyan anna".
Duk inda zakaje kaje zaka fito lafiya Insha Allah. Wata masifa ba zata same ka ba, kai ba kai bama har iyalenka babu su ba gamo da masifa a wannan ranar da yardar Allah.