Tasirin Shafa Turare A Jiki Ga Matan Aure |
Kamshi yana sanyawa mijinki yaji babu abinda yakeso irin yaji shi tare da ke. Ba kamshin jiki ne kadai yake da tasiri ba, harda kamshi na cikin gida.
Kamshi wani abune da yakeda matukar muhimmanci ga mace da namiji. Amma ba kamar kamshi agun 'ya mace yanada matukar muhimmanci. Don haka kada kice zaki rinka zama jikinki baya tareda kamshi. Domin kamshi yana daga cikin abinda yake tayar da sha'awar mace a gurin namiji, shiyasa addini yayi hani ga mace ta shafa turare a lokacin da zata fita. Wannan kamshin yana sanyawa mace ta samu babban matsayi awajen maigidanta.
Kamshi yana sanyawa mijinki yaji babu abinda yakeso irin yaji shi tare da ke. Ba kamshin jiki ne kadai yake da tasiri ba, harda kamshi na cikin gida. Ki rinka yin amfani da turaren wuta da tsintsiyar kamshi ko room freshner ko kuma duk wani abunda ke sanya wuri yayi kamshi.
'Yar uwa ki kula da kamshin jikinki, rashin jin kamshi daga gareki yana haddasa tsana gun mijinki. Yakan sanya yaji yana kyamatar ki, ya kuma kasa sakin jiki a lokacin da kuka kebanta. Domin haka sai a kula.
Bakar Humra
1. Mahala
2. Farce, hawi
3. Turaren sandal
4. Madarar turare kamar kala uku
5. Turaren babur ko aladin
Zaki dake mahala ko aladin, ki dauko mahala da hawi da farce ki tankade su ki hade guri guda, sai ki dauko wadannan turarukan ki hada guri guda, sannan ki kawo dakakkun kayan ki zuba akansu, zakiga sunyi kasa, shine yake saka tsamawa. Amma farcen sai kin wanke kin soya, idan ba dakakke bane kika samu.
Farar Humra
2. Madarar matan aure
3. Ambar
1. Hawi
4. Miski cokali hudu
5. Ruwan turaren matan aure
Da farko zaki daka hawi ya daku sosai sannan ki dauko kaskon ki, ki soya sama-sama kar ki barshi ya kone, Idan kuma bai soyu ba wari yake. Sannan sai kuma ki cika ambar da miski su daku, sai ki zuba acikin mazubi ki zuba madarar turaren matan aure, ki zuba sauran kalolin madarar turaren.
Turaren Wuta
1. Halud 3kg sandal 1kg
2. Hawi half kg
3. Farcen gwangwanin tumatir
4. Miski cokali uku
5. Sarki turaren babba 1
6. Binta sudan 1
7. Hafsa 1
8. Bokur 1
9. Kafi-kafi 1
10. Assassarubiya 1
11. Oassion 1
12. Massarubiya 1
13. Ladus sahi 1
14. Onte man shawil
15. Sanyin turaren cheri
16. Karamin sandal 1
17. Madarar turaren ambar.
Da farko zaki daura farce a wuta da ruwa, idan ya tafasa na tsawon minti talatin, sai ki wanke da omo da soson waya. Idan ya wanku sai ki baza ya bushe sannan ki daka shi sama-sama. Sai ki daura tukunya a wuta ki zuba zuma gwangwani biyu (2) da ruwa cokali takwas (8). Idan ya narke yayi ja ya tsinko yayi tsululu sai ki zuba halud da hawi da sandal ki cigaba da jujjuya su sosai. Bayan ya soyu da ruwan zuma sai ki juye a babban baho, sannan ki dauka sauran turaren cheri ki juye akai. Sai ki cakude ki bari yayi minti ashirin (20) sannan ki daka miski kar yayi laushi sosai, ki zuba. Ki daka hawi shima kar yayi laushi sosai ki zuba aciki. Sai ki zuba madarar turaren wuta duka, ki zuba farce shima ki jajjaga shi. Ki rufe shi tsawon awa 48 sannan ki zuba a kwalba ko roba.
Kulacca
1. Body lotion
2. Miski na roba
3. Garin ambar
4. Humra
5. Turare kala biyar 5
Ki hada humra da garin ambar ki daka su suyi laushi. Sai ki hadesu guri guda da turarenki ki zuba acikin manki lotion. Sai ki rufe yayi kamar awa uku (3) sannan ki fara amfani dashi.