Tarihin Bikin Ranar Masoya (RANAR VALENTINE)

Tarihin Bikin Ranar Masoya (RANAR VALENTINE)
Tarihin Bikin Ranar Masoya (RANAR VALENTINE)

Asalin bikin Ranar Masoya na daga bukukuwan Romawa a lokacin da suke kan addinin maguzanci fiye da karni goma sha bakwai da ya wuce


Ranar masoya, wacce kuma ake kira Saint Valentine's Day ko kuma idin Saint Valentine, ana bikin kowace shekara a ranar 14 ga watan Fabrairu. Al'adar, ta zama gagarumin bikin al'adu, addini, da kasuwanci da soyayya a yankuna da dama na duniya.


Akwai wata al'adar cewa Paparoma Gelasius na daya ya kafata a shekara ta 496 AD don yin bikin ranar 14 ga Fabrairu don girmama Saint Valentine na Rome, wanda ya rasu a wannan ranar a AD 269.


Ranar soyayya ba ranar hutu ce ta jama'a a kowace ƙasa ba, kodayake ranar Biki ce a hukumance a cikin haɗin gwiwar Anglican da Cocin Lutheran. Yawancin sassan Cocin Orthodox na Gabas kuma suna bikin ranar Valentine a ranar 6 ga Yuli don girmama shugaban Roman Saint Valentine, da kuma ranar 30 ga Yuli don girmama Hieromartyr Valentine, Bishop na Interamna (Terni na zamani).


Asalin bikin Ranar Masoya na daga bukukuwan Romawa a lokacin da suke kan addinin maguzanci fiye da karni goma sha bakwai da ya wuce. bikin ya samo asali ne daga akidar Romawa cewa wai wata macen kyarkeci ta taba shayar da Romulus, wanda ya assasa garin Rome nono, kuma hakan ya ba shi Karfin gaske da kuma hikima ta musamman.


Romawa sun rika yin gagarumin bikin murnar zagayowar wannan rana a tsakiyar wata Febreru na kowace shekara.


A lokacin bikin, ana yanka kare da akuya, a inda kartin matasa, majiya karfi za su shafe jikinsu da jinin, sannan, su wanke jinin da madara. Daga nan, sai su jagoranci faretin zagaya gari a kan tituna, suna rike da fatun da za su bugi duk wanda ya fado masu. Matan Romawa suna fada wa wadannan matasa don a buge su, kuma hakan yana faranta masu rai saboda imanin da suka yi cewa yana maganin matsalar rashin haihuwa.


An ce Valentine sunan wani malamin kiristoci ne wanda ya mutu a dalilin cutarwar Claudius, shugaban Gothic a shekarar 296 CE. A shekarar 350 CE an gina coci a wurin da ya mutu, domin a rika tunawa da shi. Da Romawa suka shiga cikin kiristanci, sun ci gaba da bikin soyayya, illa iyaka, sun canza shi daga bikin soyayyar ruhi irin na muguzanci zuwa bikin shahidan soyayya don tunawa da Valentine, kasancewar, a cewar su, ya yada kauna da soyayya da zaman lafiya, abin da kuma ya kai shi ga rasa ransa.


A wani kaulin kuma, an ce bikin ranar Valentine ya samo asali ne daga lokacin da Romawa suka shiga cikin kiristanci. Sarkin Rome, Claudius II ya sanya dokar hana sojoji yin aure a karni na uku bisa hujjar cewa aure zai shagaltar da su, kuma ya kau da tunaninsu daga yaki.


Valentine ya bijire wa wannan doka, kuma ya ci gaba da daura wa sojoji aure a boye. Da sarkin ya gano, sai ya jefa shi cikin kurkuku, kuma ya yanke masa hukuncin kisa.Yana cikin kurkuku ne ya kamu da ciwon son `yar sarkin, amma a boye, duk da cewa haramun ne ya so wata mace ko kuma ya yi aure, a matsayinsa na babban malamin kirista, kasancewar dokokin kiristanci sun hana. An ce daga baya, sarkin Romawa ya nemi Valentine ya bar kiristanci, ya bauta wa gunkin Romawa, shi kuma zai mai da shi daya daga cikin makusantansa kuma ya aurar masa da `yarsa.


Kasancewar Valentine ya ki yarda da haka, an kashe shi a ranar 14 ga Febreru 270 CE, a daren 15 ga watan Febrerun da aka saba yin bikin Lupercalis. Daga nan aka canza sunan bikin ya koma ranar tunawa da Valentine, ko dai saboda dagewar da ya yi a kan kiristanci, ko kuma saboda goyon bayan da ya nuna wa sojojin da suka fada cikin soyayya, har hakan ya kai shi ga rasa ransa.


Daga nan, sai Pope, shugaban kiristocin da ya gaji Saint Peter, ya mai da ranar 14 ga Febreru 270 CE a matsayin ranar bikin soyayya, kuma ya shar’anta wa duk kan kiristoci murnar zagayowar wannan rana a kowace shekara.


Da ma Allah (Madaukaki) Ya ba da labarin yadda kiristoci ke daukar malamansu a matsayin abin bauta, da yadda su ke bin abubuwan da suka halatta ko suka haramta masu sau da kafa, ba tare da neman dalili a cikin littafinsu ba.


Abubuwan Lura Dangane Da Ranar Valentine 

Asalin bikin ranar Valentine daga Romawa ne wadanda ke bin akidar maguzanci. A wajensu, biki ne da ke nuna soyayyar da su ke wa gunkinsu mai suna ubangijin soyayya.


Tarihin wannan biki a wajen Romawa ya kunshi tatsuniya da surkullen da duk wani mai hankali zai karyata, ballantana kuma Musulmin da ya san abin da ya ke yi. Hatta ma a wajen kiristoci, akwai sabani mai yawan gaske A tsakanin malamansu dangane da gaskiyar alakar Valentine da wannan biki.


Biki ne da ya kunshi kamanceceniya da mush*rikan Romawa da kuma tarayya da kiristoci. Yin kamanceceniya da kaf*irai ko tarayya da su a cikin addininsu ko akidarsu ko ibadarsu ko wata al’ada da ta kebanta da su, haramun ne kamar yadda manyan malaman musulunci suka bayyana.


 Saliadeen Sicey ✍️

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post