Ta Ya Ake Gane Mace 'Yar Iska?

Ta Ya Ake Gane Mace 'Yar Iska?
 Ta Ya Ake Gane Mace 'Yar Iska? 


Mace mai yawo, akwai matan da suna gaban iyayen su amma kuma basa zama, kullum suna yawo zuwa gidan shakatawa ko hotels, ko shagunan samari, irin wannan matan suma ana yi musu kallon 'yan iska


Alamomin gane mace yar iska, wannan ba abune mai sauki ba. Yau darasin namu zai karkata ne kan yadda ake gane mata 'yan iska. Koda yake naji wani masani yace ita mace 'yar iska a fili yake kowa ya sani. Ina iya cewa eh hakane, amma dai akwai wasu abubuwa wanda idan mutum bai sani ba bazai iya ganewa ba. 


ya ake gane mace 'yar iska

Shin wacece yar iska? Akwai abubuwan dake sa ake danganta mace da suna yar iska, ya danganta da abinda mace ke yi dake sa a kirata da 'yar iska. Zan kawo muku wasu daga cikin dabi'u da halayen da mace ke yi wanda kan iya sa har a kira ta da sunan yar iska. 


Galibi mace mai zaman kanta wacce ta bar iyayenta taje tana zaune da kanta tana kula da kanta da bukatun kanta ba tare da aure ba kuma ba iyayenta ne suke yi mata ba wannan ana yi mata kallon 'yar iska. Domin wasu mazan ne na daban suke morar ta sannan su biya mata bukatun ta, wanda ya hada da ci da sha da lafiya har da biyan kudin hanyar gidan da take zaune. 


Mace mai yawo, akwai matan da suna gaban iyayen su amma kuma basa zama, kullum suna yawo zuwa gidan shakatawa ko hotels, ko shagunan samari, irin wannan matan suma ana yi musu kallon 'yan iska, domin babu kamun kai babu tarbiyya. 


Ya ake gane mace 'yar iska, irin matan dake yin shigar banza da saka kaya masu matse jikinsu, basa Kunyar kowa kuma basa Kunyar shiga duk wani guri. Irin wannan matan komai na surar jikinsu ana gani, su hakan a wajen su kamar birgewa ne. Irin su ko fada basa ji, duk lokacin da kai kokarin ka ganar dasu za su ji kamar kana zufa su. 


Akwai wasu matan kuma su baza ka taba sanin 'yan iska bane, domin komai nasu a boye suke, kuma su basa yin shigar banza koda yaushe cikin kamala zaka gansu. Irin su ne annoba cikin al'umma. Kuma suna da tasiri wajen saurin lalata sauran yaran unguwa. Domin idan aka ganta da yaran unguwa baza ayi tunanin za ta lalata su ba. 


Wannan dai wasu ne daga cikin hanyoyi na ya ake gane mace 'yar iska, nan gaba zan kawo muku wasu hanyoyin da iyaye za su dauka don gano yadda za su shawo kan ya'yan su idan sun gano 'yar iska ce. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post