Sirrin Yadda Ake Yin Gyaran Jiki Na Musamman |
Hanyoyin Yadda Ake Yin Gyaran Jiki Na Musamman don mata
Shin wane hanyoyin zan yi amfani dasu don gyara jikina ba tare da naje wani wajen an yi min ba? Wannan itace muhimmiyar tambaya da mata ke yawan yi. Hakan yasa yau na kawo muku hanyoyin da za ku yi gyaran jiki cikin sauki.
Gyaran Jiki Na Daya 1
Wannan salon gyaran jiki ne da ake yin sa dake sa fata tayi laushi da sheki. Idan kika samu wadannan abubuwa kamar haka;
- Lalle
- Kurkur
- Madara ta ruwa
Zaki hade wadannan kayan hadin guri guda sai ki kwaba su ki shafe jikinkı da fuskarki. Zaki yi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki, sai ki murje sannan sai ki shiga wanka. jikin yana yin kyau yayi sheki.
Gyaran Jiki Na Biyu 2
Wannan hadin shi ake cewa 'taskira'. Domin yana gyara fata sosai tares da saka laushi fatar, ku samu wannan abubuwan kamar haka;
- Kurkur
- Dilka
- Zuma
- Kwai
- Lemon tsami
Ki hada su guri guda ki samu ruwa ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa. Sa ki shafe fuskarki. Idan kuma har da jiki kike so sai ki shafa har a jikin. Bayan awa daya sai ki shiga wanka. zakiga yadda jikin ki zai goge.
Gyaran Jiki Na Uku 3 (AKORI BLEACHING)
Wannan hadin gyara fata yana da kyau sosai, idan so kike ki yi haske fatar ki tai sheki, Fata tayi laushi da sheki, ki samu wannan abubuwan;
- Lalle
- Gwaiduwar kwai
- Manja cokali uku
- Kurkur
Sai ki kwaba su guri guda ki shafe jikinki zuwa awa guda, sai kiyi wanka da ruwa zalla. Sannan ki jika dilka da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita. Sai kuma yin wanka.
Kyan Fuska (MAI WALKIYA)
Idan kina son ki gyara fuskarki ta yi kyau da sheki kina iya yin wannan hadin,
- Dettol
- Sabulun ghana
- Garin zogale
- Farar albasa
Sai ki hade su guri guda ki daka su a turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska. Zakiga yadda fuskarki zatayi kyau. Wannan hadin yana da kyau sosai musamman ga yan mata dake son birge Samari.
Gyaran Fuska ('YAR SUFUL-SUFUL)
Wannan wani hadine wanda yake sa fuska tayi haske da annuri sannan kuma ta kore kurajen fuska.
A samu bawon kankana (cikin bawon) sai a rinka goge fuska dashi. Yana gyara fuska tayi sumul.
Wannan sune hanyoyin da ake gyara jiki, da fatan kun amfana, sannan nan gaba zan kawo muku karin bayani kan yadda ake gyara fata musamman ga matan dake shirin yin aure.