Sirrin Gyaran Jiki Da Gyaran Nono
![]() |
Sirrin Gyaran Jiki Da Gyaran Nono |
Matan dake son gyaran nono da rage tumbi ga wasu hanyoyi na musamman da ake yin magani
Yau na kawo muku hanyoyi biyu da za ku bi don gyaran nono da gyaran tumbi, musamman ga matan dake korafin suna fama da matsalar zubewar nono da girman tumbi.
Gyaran Nono
Macen da takeso kada nononta ya fadi, koda yaushe nononta ya zama a tsaye. Idan ma budurwa, ko matar aure, ko bazawara, to ga shawara;
- Kumfar maliya
- Kaltufa
- Hulba
Zaki samu garin hulba ki tafasa, sai ki dan debi ruwan ki gasa nonuwanki dashi. Ki samu kumfar maliya ki nikata ta zama gari. In tayi laushi sosai sai ki zuba ruwan kaltufa aciki, sai ki kwaba ki shafe nonoki dashi idan zaki kwanta. Sannan kisamu rigar nono mai karfi ki saka (mai kama nono) ki kwana da ita. In gari ya waye sai kisa ruwan dumi ki wanke. Bayan kin wanke sai ki samu man hulba da ridi ki shafe nononki dashi. Zaki sha mamaki in Allah ya yarda.
Gyaran Tumbi
Macen da bata son aganta da tumbi, kinfinson ki zama 'yar dagwas-dagwas ki zama dai-dai wa dai-dai. Ki samu kaltufa ki rinka zubawa acikin ruwan dumi kina sa kanunfari, ki sha sau biyu a rana; da safe da daddare.
Kuma kina shafawa tumbi man na'a-na'a. Musamman idan zaki kwanta bacci. 'Yar uwa zaki sha mamaki da yardar Allah, sai dai anyi hakuri don abin bana gajere bane.
Leave Comments
Post a Comment