Sirrin Addu'ar Ismullahil A'azim

Sirrin Addu'ar Ismullahil A'azim
Sirrin Addu'ar Ismullahil A'azim 


Duk irin yanayi daka samu kanka na kuncin rayuwa ko halin talauci ko rashin lafiya tayi tsanani an rasa gane irinta. Ko neman aiki ko neman mijin aure ya gagara, ko haihuwa


Wannan addu'ar akanso akalla in ka samu hali kayi ta kullum, ko kuma idan baka samu hali ba to kayi ta duk lokacin da ya samu, duk sati ne, ko wata koma shekara, koda sau daya ne ba wani abu da zaka roki Allah da wannan addu'ar face ya amsa maka cikin yardarsa sai ya biya maka bukata.


Don haka anaso cikin dare ka tashi kayi nafila raka'ah biyu ko hudu ko takwas. Bayan kinyi istigfari kinyi hailala da salatin annabi da yaqini a zuciyarki Allah zai karbar miki addu'a. Ga addu'ar kamar haka;


" اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِاسمك العظيم الذي إذا دعيت به أجبت وَإِذَا سُئِلْتَ به أُعْطِيتَ أسْأَلُك بأني أشهد أنك أنت الله لا إله إلا أنْتَ الْأَحْدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُن له كفوا أحد أنْ تَغْفِرَ لَنَا ذُنُوبَنَا وَتَيَسَّرَ أَمُورَنَا

وَتُقَصِّيَ حَوَائِجَنَا وَتُصْلِحَ أَحْوَالَنَا إِنَّكَ أَنْتَ الْكَرِيمُ"


"Allahumma inni as'aluka bi ismikal azim, alladhi iza du'ita bihi ajabta wa iza su'ilta bihi a'adaita, as'aluka bi anni ash hadu annaka antallahu la ilaha illa antal ahadus samadul ladhi lam yalid walam yulad, walam yakun lahu kufwan ahad. An tagfir lana zunubana wa tayassir umurana wa taqdi hawa'ijana wa tuslihu ahwalina innaka antal karim".


 Addu'ar Ismullahil A'azim II

Duk irin yanayi daka samu kanka na kuncin rayuwa ko halin talauci ko rashin lafiya tayi tsanani an rasa gane irinta. Ko neman aiki ko neman mijin aure ya gagara, ko haihuwa. Kai duk irin abinda kake nema gurin Allah SWT koma mene kayi imani cewa Allah zai amsa maka.


Kuskurene kazo kana yin addu'a amma kana kokwanto ko Allah ba zai amsa ba. Saboda annabi SAW yace; "ku roki Allah da tabbacin zai amsa muku". Don haka lokacin daka samu kanka cikin damuwa ka tashi ko ki tashi cikin dare kiyi nafila raka'ah biyu ko hudu koma duk yadda ya sauwaka. Bayan sallama sai kiyi istigfari da salatin annabi adadin da ya sauwaka sannan sai ki dauki wannan addu'ar kamar haka:


بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَانِ الرَّحِيمِ اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ يَا مُؤْنِسَ كُلَّ وَحِيدِ يَا قَرِيبًا غَيْرَ بَعِيدٍ, يَا شَاهِدًا غَيْرَ غَائِبِ يَا غَالِبًا غَيْرَ مَغْلُوبِ يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ يَا بَدِيع السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يَا ذَالْجَلَالِ وَالإِكْرَامِ أَسْأَلُكَ بِاسْمِكَ بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ الَّذِي عَنتْ لَهُ الْوُجُوهُ وَخَشِعَتْ لَهُ الْأَصْوَاتُ وَ وَجِلَتْ لَهُ الْقُلُوبُ أَنْ تُصَلِّي عَلَى مُحْمَدٍ وَعَلَى آلِهِ وَأَنْ تُعطيني كَذَا وَكَذَا إِنَّكَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قدير"


"Bismillahir rahmanir rahim. Allahumma inni as'aluka ya mu'nisu kulli waheed, ya qariban gaira ba'id, ya shahidan gaira gaib, ya galiban gaira maglub, ya hayya ya qayyum, ya badi'us samawati wal ardi ya zal jalalu wal ikram, as'aluka bi ismika bismillahir rahmanir rahim, alladhi anatu lahul wujuhu wa khashi'at lahul aswat wa wajilat lahul qulıb, ap tusalli ala Muhammadin wa ala alihi wa an tu'dini kazha wa kazha (sai ka fadi bukatar ka) innaka ala kulli shai'in qadir".


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post