Halayen mata nagari |
Matar da ta dauki aure a matsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin rayuwa kawai ba. Wannan shine halayen mata tagari
Menene halayen mata nagari? Wannan tambaya ce da kullum Samari ke yi don sanin irin Macen da za su aura ko tana da irin wannan halayen. Wannan yasa na kawo muku wasu daga cikin halayen mata na kirki wanda duk namijin kirki ke buri da fatan aura.
Halayen Mata Nagari
Mace tagari ita macen da kowane namji ke buri da fatan aura. Su halayen Mace ta gari ana iya gane su tun kafin aure, wasu halayen kuma ba'a iya gane su har sai bayan aure. Ga kadan daga cikin su kamar haka;
1. Matar dake son mijinta da kulawa dashi bayan aurensu fiye da yadda take son shi tun lokacin yana zuwa hira gidansu
2. Matar dake kishin mijinta. Domin Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: “duk matar da bata kishin mijinta ba za ta shiga Aljannah ba”.
3. Matar da ta dauki aure a matsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin rayuwa kawai ba. Wannan shine halayen mata tagari
4. Matar da ta dauki mijinta a matsayin abokinata, yayanta, almajirarsa, kuma abokin shawararta.
5. Mata tagari itace wadda bata zagin mijinta, bata cin mutuncinsa, bata cin zalinsa, bata ha’intarta koda a bayan idonta ne
6. Itace wacce ke zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa. Wanda idan ta fahimci halayen mijinta, take hakurin zama da shi tare da kyautata masa domin neman rahamar Allah Ta’ala.
7. Mata tagari itace wacce idan za ta yi magana da mijinta, za ta fadi gaskiya babu yaudara ko karya a cikin zancen ta.
8. Mace Tagari itace wacce ta dauka a zuciyarta cewa: Iyayen mijinta, Iyayenta ne. ‘Yan uwanta ma ‘yan uwansa ne, kuma dangin mijinta danginta ne.
9. Ita ce wadda ke daukar cewa farin cikin mijinta shine farin cikinta kuma matsalar sa, itama tata ce. Halayen Mata tagari Kenan
10. Mata tagari ita ce wadda ke kokarin kiyaye sirrin mijinta, kuma take kokarin kare masa mutuncinta koda a wajen ‘yan uwanta ne, tare da hikima da fahimtarwa.
11. Ita mata tagari bata fifita wani akan mijinta, kuma bata tauye masa darajarsa. Tana bawa kowanne gefe nasa hakkin kamar yadda shari’ah ta tanada. Wannan shine halayen mata tagari
12. Itace wadda ta tanadi ruwan afuwa da hakuri a cikin zuciyarta domin kashe wutar tashin hankali da bacin rai a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninta da mijinta.
13. Itace a kullum take kokarin tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin Islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasara ba. Mace tagari Kenan
14. Itace wadda ke zaune da mijinta komai dadi komai wuya ba za ta daina nuna masa soyayya ba wai don ya fara yankwanewa ko kuma karfinsa yafara raguwa.
15. Itace wacce ke bawa mijinta yabo a duk lokacin da yayi kwalliya ko kuma ya yi mata wata kyauta.
Mata tagari bata raki bata ihu don mijinta bai yi mata abinda ranta ke so ba. Sai dai duk wanda ya kawo mata za ta yaba ta yi godiya. Wadannan sune halayen mata nagari. Allah Yasa mata su gane, su sauke hakkinsu na kulawa da mazajensu Ameen.